Ministan Kuɗi na Rasha, Anton Siluanov, ya bayyana a tattaunawar taron ƙasashe 20 mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya, ta G20, wadda Amurka ta ɗauƙi nauyi a North Carolina.
Sai dai bayyanarsa ta jefa ministoci da jami’an ƙasashen Turai cikin fushi da takaici.
Bayyanar Siluanov a taron da aka gudanar a Asheville a ranar Litinin ita ce karon farko da ministan ya halarci taron G20 da kansa tun bayan da Moscow ta ƙaddamar da mamayar Ukraine a shekarar 2022.
An nada Siluanov minista tun 2011.
Ya yi ganawa da sakataren kuɗi na Amurka, Scott Bessent, inda ma’aikatar kuɗi ta Rasha ta ce sun tattauna kan haɗin gwiwar tattalin arziki da yayi dai-dai da tsarin G20.
Wani jami’in Amurka ya ce tattaunawar ta fi mayar da hankali ne kan shirin zaman lafiya na Shugaba Donald Trump akan Ukraine.
-
Gwamnati za ta biya mutanen da ta rusawa gidaje a Yamai diyya
-
Kasar Norway za ta dakatar da kiwon kajin Broiler
-
An dawo da zaman lafiya a Niamey bayan yunkurin tawaye a rundunar sojin Nijar
Da aka tambaye shi kan gayyatar Siluanov, Trump ya shaida wa manema labarai cewa: “Muna son mu zauna lafiya da kowa. Ɗaya daga cikin dalilan da na ke samun nasara shi ne na zama lafiya da kowa.”

Sai dai jami’an Turai sun soki wannan mataki.
Ministan Kuɗi na Poland, Andrzej Domanski, ya ce bai ji daɗin ganin Moscow ta samu wakilci ba, duk da ya amince cewa ƙasar da ta ɗauki nauyin taron tana da hakkin gayyatar baƙi.
“Ba za mu iya amincewa da Rasha ba. Suna yin ƙarya a kullum, kuma dole sai an yi taka tsantsan sosai idan ana tattaunawa da su,” in ji shi a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Ya jaddada cewa Rasha ce ta kai farmaki a yakin da ta keyi da Ukraine.
“Saboda haka a gare ni, zai yi matukar wahala in yi wata tattaunawa da Rasha.”
Ministan Kudi na Jamus, Lars Klingbeil, ya ce matakin Amurka na maraba da Siluanov tamkar aika “sako ne mai firgitarwa.”
Ya kuma ce Turai na shirin fitar da sabon kunshin takunkumi kan Rasha, sannan tana fatan hadin gwiwa da Washington kan wadannan matakai.
Jami’an Turai sun ce ministocin kudi da gwamnoni na bankunan Turai sun ki amincewa su dauki hoto tare da Siluanov bayan taron na G20. A karshe an dauki hoton ba tare da ministan Rasha ba.
Da aka tambayi mai magana da yawun Fadar White House, Kush Desai, kan halartar Siluanov, ya shaida wa AFP cewa gwamnatin Trump ta na aiki da Rasha ne domin cimma yarjejeniya da za ta “dakatar da kashe-kashe wanda shugaban ya yi Allah wadai da shi.”