Wani mataki na tarihi da kasar Norway ta dauka a fannin kyautata rayuwar dabbobi na gab da kawo gagarumin sauyi a bangaren kiwon kaji.
Wani haɗin gwiwar babban kamfanin sarrafa nama da kwan kaji mafi girma a daukacin kasar Norway mai suna (Nortura SA), da Kungiyar masu noman da samar da nama a Kasar (KLF) ne suka amince da waɗannan gyare-gyare a daukacin masana’antar kiwon kajin kasar.
Karkashin sabuwar yarjejeniyar, za a daina amfani da nau’in kaji na (Ross 308), nau’i mafi saurin girma da aka fi amfani da shi a nahiyar Turai, kafin ranar 31 ga Disamba, 2027.
Nau’in kajin na Ross 308, an gudanar da sauyin halitta a kansu ne domin su kai nauyin yanka a cikin makwanni ƙalilan, lamarin dake shafar bugun zuciyar su fiye da kima, baya ga raunana garkuwar jikinsu.
Sakamakon haka, da yawa daga cikin kajin suna fama da radadi marar misaltuwa yayin tafiya ko tsayuwa, haka kuma sauran matsalolin lafiya a dan takaitaccen lokacin rayuwarsu.
- An kashe mutum 96 a Saudiyya tsakanin watan Janairu zuwa Yuni, ciki har da ɗan Najeriya
-
Nepal: An fara aikin ceto ma’aikata 933 da ake zargin ambaliyar ruwa ta binne
A watan Agusta na shekarar 2022, kamfanin kiwon kaji na Norsk Kylling a kasar Norway, ya zama kamfani na farko a duniya da ya sauya daukacin kiwon sa zuwa nau’in da ke girma a hankali, ƙarkashin wasu ƙa’idojin wani tsarin kiwo da aka yi wa laƙabi da Better Chicken Commitment (BCC).
Nasarar da kamfanin ya samu ta tabbatar da cewa kiwon kaji masu ingancin lafiya na yiwuwa tare da samar da riba mai gwabi ta fuskar kasuwanci.
Yarjejeniyar ta kuma samar da sabuwar fasahar gane halittar dake cikin kwai gabanin ƙyanƙyashewa, wadda zata fara aiki a ƙasa baki daya daga ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2027.
To ko yaya lamarin zai shafi masu sana’ar kiwon kajin Broiler a Najeriya?
Ga manoma da masu kiwon kaji a tsarin kasuwanci a Najeriya, musamman wadanda ke amfani da nau’ikan kaji masu saurin girma kamar Ross 308, wannan mataki na kasar Norway yana dauke da sakonni da darussa da ya kamata su yi la’akari dasu.
Na farko Kasuwannin duniya suna kara mai da hankali kan inganci da lafiyar dabba, ganin yadda cin abinci da aka yi amfani da hanyoyin zamani wajen gina shi ke shafar lafiyar dan adam.
Duk da cewa kaji masu saurin girma suna da saurin kawo kuɗi, sai dai galibi suna fuskantar matsalar rashin kwarin ƙashi da mutuwar fuju’a, yayin da nau’ikan kajin da ke girma a hankali ke zuwa da sabanin hakan.