A cewar mujallar, bikin bayar da kyaututtukan karo na 70 zai gudana ne a ranar 26 ga Oktoba, inda za a bayyana sunayen waɗanda suka lashe kyaututtuka daban-daban, ciki har da gwarazan ’yan wasa na maza da mata.
- Sanwo-Olu ya yabawa ƙungiyar LGAN kan bunƙasa wasannin mata
- Lagos za ta karɓi bakuncin bikin bayar da kyaututtukan CAF na 2026
- An cire Najeriya daga Gasar WAFU B ta U17, kuma ta rasa tikitin Zuwa AFCON da Gasar kofin duniya
Ƙa’idojin da aka tsara bisa muhimmancinsu sun haɗa da bajintar ɗan wasa a kashin kansa, inda ake duba ƙwarewarsa, irin tasirin da ya yi a wasanni da kuma gudummawar da ya bayar wajen nasarar ƙungiyarsa.
Ƙa’ida ta biyu ita ce nasarorin da aka samu tare da ƙungiya, inda alkalai ke la’akari da kofunan da ɗan wasa ya lashe tare da ƙungiyarsa ko tawagar ƙasarsa a lokacin da ake tantancewa.
Ƙa’ida ta uku kuwa ita ce ɗabi’a, mutunci da wasan cikin adalci, inda ake duba yadda ɗan wasan ke nuna girmamawa ga abokan hamayya, alkalai da kuma bin ƙa’idojin wasa.
’Yan jarida 100 ne ke kaɗa ƙuri’a wajen zaɓen gwarzon ɗan wasa na maza, yayin da ’yan jarida 50 ke zaɓen gwarzon ɗan wasa na mata. Kowanne alƙali na tsara ’yan wasa goma bisa ƙa’idojin da France Football ta gindaya.