Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne bayan ganawa da tawagar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin mai ɗaukar nauyinta kuma Iyalode ta Legas, Cif Bintu-Fatima Tinubu.
- NAOWA ta bukaci ƙara wayar da kai kan kansar mama da lafiyar kwakwalwa
- Lagos za ta karɓi bakuncin bikin bayar da kyaututtukan CAF na 2026
Gwamnan ya ce yana farin cikin ganin shirye-shiryen da ke samar wa mata damammaki su bunƙasa ƙwarewarsu, yana mai cewa Jihar Legas na alfahari da tallafa wa Najeriya wajen karɓar bakuncin gasar All Africa Challenge Trophy ta 2026.
Za a gudanar da gasar daga ranar 2 zuwa 7 ga Nuwamba a filin wasan golf na IBB International Golf and Country Club da ke Abuja.
Gasar za ta haɗa mata masu wasan golf daga ƙasashen Afirka 30, inda kowace ƙasa za ta tura wakilanta domin fafatawa.
Sanwo-Olu ya yi wa tawagar Najeriya fatan alheri yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gasar.