Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da fashi da makami, tare da kwato wasu daga cikin kayayyakin da aka sace a Birshi Gandu, cikin birnin Bauchi.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar 18 ga Oktoba, 2026, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 17 ga Oktoba da misalin ƙarfe 10:15 na safe, bayan wasu mutum huɗu, maza biyu da mata biyu, sun kai rahoto ofishin ’yan sanda na sashen E-Division.

Sanarwar ta ce waɗanda abin ya shafa sun bayyana cewa wasu mutane uku ɗauke da wuƙaƙe da adduna sun kutsa cikin harabar gidansu da ke ɗauke da Cozy Resort Hotel, lokacin da suke barci, inda suka ƙwace kayayyakin da suka haɗa da wayoyin Samsung Galaxy S22 da S23, Redmi Note 14, iPhones, iPads, kwamfutar tafi-da-gidanka ta Lenovo, kwamfutar hannu ta Samsung da sauran kayayyaki na miliyoyin naira.

Rundunar ta ce jami’an ’yan sanda na sashen E-Division Yelwa, tare da taimakon wasu mazauna yankin, sun bi diddigin ɗaya daga cikin wayoyin da aka sace, lamarin da ya taimaka wajen kama waɗanda ake zargi biyu, Abdulshakur Adamu mai shekara 20, wanda aka fi sani da Dan Oga, da Rabiu Usman mai shekara 21.

A cewar sanarwar, waɗanda ake zargin sun amsa laifin yayin tambayoyi, inda suka bayyana cewa sun haɗa baki da wani Kabiru, wanda aka fi sani da KB, mazaunin Birshi Gandu, wajen aikata fashin.

’Yan sandan sun kuma kwato wayoyin hannu guda uku, na’urorin caji guda biyu, na’urar sauraron sauti guda ɗaya da kebul na USB, an kuma samu wata wuƙa da aka ajiye a matsayin shaida.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin miƙa lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike, da kama wanda ya tsere da kuma gano sauran kayayyakin da aka sace, kafin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *