Obi ya bayyana hakan ne bayan ganawa da wasu ’yan Najeriya da ke zaune a Manchester, Birtaniya, inda ya ce ya saurari damuwarsu game da halin da ƙasar ke ciki tare da jin daɗin yadda suke nuna sha’awar gina Najeriya mai kyau ga kowa.
- Sanwo-Olu ya yabawa ƙungiyar LGAN kan bunƙasa wasannin mata
- NAOWA ta bukaci ƙara wayar da kai kan kansar mama da lafiyar kwakwalwa
- ’Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargi da fashi da makami a Bauchi
Ya ce Najeriya na fuskantar manyan ƙalubale, kuma bai kamata ’yan ƙasar su ja da baya wajen fuskantar aikin da ke gabansu ba, inda jaddada cewa lokaci ya yi da za a ɗauki matakan da suka dace domin samar da sauyi mai ma’ana.
Obi ya danganta matsalolin ci gaban ƙasar da yaƙe-yaƙen cin hanci da rashawa da kuma gazawar shugabanci tsawon shekaru, ya ce Najeriya na daga cikin ƙasashen da Allah ya yi wa arzikin albarkatu, amma da ba don waɗannan matsaloli ba, da ta kasance cikin ƙasashen da suka ci gaba sosai.
Ya ƙara da cewa ci gaban kowace ƙasa yana da alaƙa da halaye, ƙwarewa, iyawa da jajircewar shugabanninta, yana mai cewa ya kamata a tunkari zaɓe mai zuwa a matsayin muhimmin mataki na ceton ƙasa, ba kawai wani zaɓe na yau da kullum ba.
Obi ya ce alhakin samar da “Sabuwar Najeriya mai yiwuwa ne” kuma ya rataya ne a kan dukkan ’yan ƙasar.