Taron Lafiyar Al’umma (Health Equity Conference) na shekarar 2026, wanda gidauniyar OneBarrow International Limited ta shirya, ya kammala zamansa na kwanaki biyu a Abuja, tare da kira da a inganta haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin kiwon lafiya, domin tabbatar da samun ingantaccen magani cikin adalci a faɗin Najeriya.

Taron ya samu halartar wakilan hukumomin dake kula da harkokin kiwon lafiya, da ƙungiyoyin ƙwararru, da masu samar da ayyukan lafiya, da gwamnati, da kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki, domin tattauna hanyoyin inganta haɗin gwiwa tsakanin cibiyoyin lafiya da ma’aikatan dake cikinsu.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken “Haɗin Gwiwa Wajen Kula da Marasa Lafiya a Matsayin Ginshiƙin Samar da Adalci a Kiwon Lafiya.” Mahalarta taron sun yi nazari kan matsalolin dake hana marasa lafiya samun kulawa mai inganci da ci gaba daga matakin farko na neman magani zuwa kammala jinya.

A yayin taron, an yi amfani da labarin wata mara lafiya ta ƙirƙira mai suna Amina, domin nazarin matsalolin da marasa lafiya ke fuskanta tun daga samun damar zuwa asibiti, da gwaje-gwaje, da karɓar magani, da tura su zuwa wasu cibiyoyin lafiya, da kwantar da su a asibiti da kuma bibiyar lafiyarsu bayan an sallame su.

Taron ya mayar da hankali kan fannoni biyar da suka haɗa da dokoki da sa ido, da kuɗaɗen gudanar da lafiya, da samar da ayyukan kiwon lafiya, da ma’aikata da fasahar zamani, da kuma shigar al’umma cikin harkokin lafiya.

Daga cikin matsalolin da aka gano akwai rashin ingantaccen tantance marasa lafiya,da matsalar ingancin gwaje-gwaje, da tsadar magunguna, da ƙarancin ma’aikatan lafiya, da rashin ingantaccen tsarin tura marasa lafiya daga asibiti zuwa wani, da kuma matsalar kula da su bayan an sallame su.

An kuma gano ƙarancin samun ayyukan lafiya a yankunan karkara, da matsalolin kuɗaɗen jinya, da rashin ingantaccen musayar bayanan marasa lafiya.

Mahalarta taron sun bayyana cewa, matsala a wani sashe na tsarin kiwon lafiya na iya kawo cikas ga samun magani a wani sashe.

Misali, ana iya tura mara lafiya zuwa wani asibiti amma ya kasa zuwa saboda rashin kuɗin mota, da rashin kuɗin magani, ko ƙarancin ma’aikata ko kuma rashin isassun bayanai game da yanayin lafiyarsa.

Bayan tattaunawar, taron ya tattara abubuwan da aka gano zuwa fannoni goma na shawarwari, tare da tsara wani daftarin tsarin aiwatar da shawarwarin da zai taimaka wajen danganta kowace matsala da matakan magance ta, hukumomin da abin ya shafa da kuma hanyoyin auna ci gaba.

Sai dai masu shirya taron sun bayyana cewa shawarwarin za su kasance ne domin hukumomin da abin ya shafa su duba tare da yin la’akari da su bisa ikon da doka ta ba su.

Kamfanin OneBarrow International Limited ya ce yana shirin tattaunawa da Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, da hukumomin kula da ƙwararrun ma’aikatan lafiya, da ƙungiyoyin ƙwararru da cibiyoyin kiwon lafiya domin gabatar musu da sakamakon nazarin da shawarwarin taron.

Za a kuma duba yiwuwar horas da ma’aikata, da inganta tsarin aiki da kuma amfani da fasahar zamani wajen sarrafa bayanan marasa lafiya.

Taron ya yi kira ga al’umma, da ƙwararrun ma’aikatan lafiya, da kamfanoni, da ƙungiyoyin farar hula, da jami’o’i da sauran masu ruwa da tsaki a Najeriya da su taimaka wajen gano matsalolin samun kulawar lafiya, da inganta tsarin tura marasa lafiya, da tallafa wa al’ummomi da ba sa samun ingantaccen kulawa da kuma wayar da kan jama’a game da rigakafi da kula da lafiya.

A wani mataki na gaba, OneBarrow International Limited na shirin gudanar da bikin bayar da lambobin yabo da liyafa na HEC 2027 Health Equity Awards & Gala, domin karrama mutane, da al’ummomi da ƙungiyoyin da suka bayar da gudummawa wajen inganta ayyukan kiwon lafiya.

Kamfanin ya jaddada cewa shirin har yanzu shawara ce da ake shirin aiwatarwa, kuma za a sanar da sharuddan zaɓen waɗanda za a karrama nan gaba.

Masu shirya taron sun ce za a auna nasarar ƙoƙarin ne ta yadda marasa lafiya za su samu sauƙin samun magani, da ci gaba da kulawa da kuma ingantattun ayyukan lafiya.

Taken taron: Mara Lafiya Ɗaya, da Tafiyar Jinya Ɗaya, da Adalci a Kiwon Lafiya Ga Kowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *