Arsenal ta tabbatar da cewa Gabriel Jesus ya rattaba hannu da ƙungiyar Barcelona kan kwantaragin dindindin.
Ɗan wasan mai shekaru 29 ya koma Gunners ne daga Manchester City a watan Yulin 2022, kuma ya buga wasanni 123 a dukkan gasa, inda ya zura ƙwallaye 32.
Ɗan wasan gaba na ƙasar Brazil ya buga wasanni 27 a dukkan gasa a kakar da Arsenal ta lashe Gasar Firimiyar Ingila, duk da cewa bai buga mafi yawan wasan kakar 2024/2025 ba saboda jinyar da yayi na raunin da ya samu a gwiwa, a watan Janairun 2025.
-
Ikpeme ya buƙaci Falconets ta doke kasar Koriya
-
Arsenal ta doke Aston Villa a Gasar Premier
-
Enugu Rangers ta tashi 1-1 da Katsina United, Barau FC 3-1 Nasarawa United…
Arsenal ta rubuta a shafinta na intanet: “Gabby ya bar mu da ƙwarewa mai yawa da ya samu daga Gasar Firimiya da kuma ɗimbin nasarori da tarihin da ya kafa a harkokin ƙwallon ƙafar Ingila.
A tsawon lokacin da ya yi da Arsenal da Manchester City, ya buga wasanni sama da 200 a Firimiya, inda ya zura ƙwallaye sama da 70, sannan ya taka rawa a lashe kofin sau 5.”
“Muna godiya ga Gabby bisa gudunmawar da ya bayar a cikin shekaru 4 da ya yi tare da mu, kuma muna yi masa da iyalinsa fatan alkhairi da nasara a rayuwarsa ta gaba.”
Kafar Sky Sports News ta ruwaito cewa Barcelona ta biya fam miliyan 8 da 600,00 domin sayan ɗan wasan gaban na Brazil.
