Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 4.43 cikin 100 a hakikanin ma’auni a zangon watanni uku na biyu na shekarar 2026, idan aka kwatanta da zangon makamancin wannan na shekarar 2025.
NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta kan kudaden shiga a zangon farko na shekarar 2026, inda ta ce bangaren manfetur da sauran bangarori suka samu ci gaba a lokacin da ake nazari.
A cewar hukumar, bangaren manfetur ya karu da kashi 7.31 cikin 100, yayin da bangaren da ba na mai ba ya karu da kashi 4.3 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
NBS ta ce kudaden shigar da Najeriya ke samu sun karu da kashi 4.43 cikin 100 a zangon na biyu na shekarar 2026, daga kashi 4.23 da aka samu a zangon makamancin shekarar 2025.
Hukumar ta kuma ce bangaren noma ya samu ci gaban kashi 4.39 cikin 100, wanda ya fi kashi 2.82 da aka samu a zangon na biyu na shekarar 2025.
Sai dai bangaren masana’antu ya samu raguwar ci gaba, inda ya tsaya kan kashi 3.96 cikin 100 daga kashi 7.46 a zangon makamancin shekarar 2025.
Bangaren ayyuka kuwa ya samu ci gaban kashi 4.6 cikin 100, daga kashi 3.94 a zangon na biyu na shekarar 2025.
-
Zan dawo da kasashen AES cikin Ecowas – Atiku
-
Babu wata ƙungiyar addinin musulunci da ta ce za ta kafa Hisbah a Jihar Filato – JNI
Dangane da gudunmawar bangarorin ga GDP, NBS ta ce bangaren ayyuka ne ya fi bayar da gudunmawa, inda ya kai kashi 56.62 cikin 100 na GDP a zangon na biyu na 2026, idan aka kwatanta da kashi 56.53 a zangon makamancin shekarar 2025.
Farfadowar bangaren mai
NBS ta ce Najeriya ta samu matsakaicin samar da danyen mai ganga miliyan 1.72 a kowace rana a zangon na biyu na shekarar 2026.
Wannan adadi ya fi ganga miliyan 1.68 da aka samar a kowace rana a zangon makamancin shekarar 2025 da ganga miliyan 0.05, sannan ya zarce ganga miliyan 1.55 da aka samar a zangon farko na shekarar 2026 da ganga miliyan 0.17.
Hukumar ta ce bangaren mai ya samu ci gaban kashi 7.31 cikin 100 a zangon na biyu na 2026, duk da cewa hakan ya yi kasa da kashi 20.46 da aka samu a zangon makamancin shekarar 2025.
A kwatankwacin zangon farko na 2026, NBS ta ce ci gaban bangaren mai ya karu da maki 4.74, daga kashi 2.57.
A tsarin kwatanta zanguna uku da juna, bangaren mai ya samu ci gaban kashi 10.91 a zangon na biyu na shekarar 2026.
NBS ta kara da cewa bangaren mai ya bayar da gudunmawar kashi 4.16 cikin 100 ga GDP din Najeriya a hakikanin ma’auni a zangon na biyu na 2026, daga kashi 4.05 a zangon makamancin shekarar 2025 da kuma kashi 3.92 a zangon farko na shekarar 2026.