Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta bai wa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, kwanaki 7 domin bayyana abin da ya faru dangane da zargin murabus ɗin Shugabanta, Ibrahim Gusau.

FIFA ta ce idan ba a ba ta amsa mai gamsarwa ba, za ta iya dakatar da Najeriya daga dukkan Gasa na FIFA da kuma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika, CAF.

Cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 1 ga Satumba, 2026, wadda sakataren FIFA, Mattias Grafström, ya rattaba hannu aka tura wa Shugaban NFF da kuma Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), FIFA ta bayyana damuwarta kan rahotannin da ke cewa Gusau ya yi murabus ne bisa umarni daga fadar shugaban ƙasa.

A cewar wasiƙar, kundin gudanarwa na FIFA ya tanadi cewa mambobi su gudanar da harkokinsu ba tare da wani matsin lamba daga waje ba, ciki har da hukumomin gwamnati.

FIFA ta buƙaci bayyanai 3 daga Gwamnatin Najeriya da kuma NFF:

  • A tabbatar mata a rubuce cewa murabus ɗin da Ibrahim Gusau ya yi na muraɗin kansa ne ba wai an tursasa masa bane daga waje.
  • Gwamnatin tarayya ta bata bayani kan abin da ya faru har ya kai ga barin muƙamin nasa.
  • A tabbatar mata cewa NFF za ta ci gaba da aiki bisa bin ƙundin tsarinta da kuma bin dokokin FIFA

FIFA ta bai wa Gwamnatin Najeriya kwanaki 7 ta miƙa mata waɗannan bayanan.

“Idan ba a bayar da bayani mai gamsarwa ba,” kamar yadda wasiƙar ta ce, “Majalisar FIFA za ta iya yanke shawarar dakatar da NFF daga dukkan gasa da harkokin FIFA da CAF nan da nan,” in ji wasiƙar.

Wasiƙar ta ƙara da cewa, idan aka dakatar da Najeriya, FIFA da CAF za su naɗa “Kwamitin Gudanarwa” na riƙo da gudanar da harkokin NFF na yau da kullum da kuma shirya sabon zaɓe bisa kundin FIFA.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rahotannin murabus ɗin Gusau da kuma mambobin kwamitin zartarwa na NFF.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *