Warin danyen mai ya mamaye al’ummomin da ke yankin Kurmin Nembe dake jihar Bayelsa, inda man ya rufe dazuzzukan mangrove, tsofaffin bishiyoyi da kuma hanyoyin ruwa da al’ummomin yankin suka dogara da su wajen gudanar da harkokin kamun kifi tsawon shekaru.
Fiye da ƙauyukan masunta 20 da ke kusa da wannan hanyar ruwa na fuskantar babbar barazana ga rayuwarsu da kuma muhalli sakamakon sabuwar malalar man.
- EFCC ta kori ma’aikata fiye da 40
- Babu wata ƙungiyar addinin musulunci da ta ce za ta kafa Hisbah a Jihar Filato – JNI
- Asusun X na Rundunar Sojin Najeriya ya sake fuskantar kutse
Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Agustan 2026, lokacin da wani jirgin ruwa mai ɗaukar kaya da ke lodin danyen mai daga wani bututun mai da ake kira kurmin manifold a wani wurin aikin mai na kurmin Creek, wanda kamfanin mai na cikin gida, Aiteo, ke gudanarwa, ya fashe.
Rahotanni sun ce fashewar ta jawo zubewar ɗimbin danyen mai cikin kogin.
Al’ummomin da abin ya shafa sun haɗa da Mile 1 da Mile 2 da Mile 3 da Roka da Williamkiri da Atonbarakiri da Korukiri da Ewelesuo da Kpongbokiri da Victorkiri da Abuja 1 zuwa 3 da Pipeline 1 zuwa 4 da wasu ƙauyuka da dama.
Ana fargabar cewa motsin ruwa sakamakon igiyar ruwa zai iya ɗaukar danyen man zuwa cikin fadamun mangrove, lamarin da ka iya yin illa ga halittun ruwa da suka haɗa da periwinkles, kaguwa da oysters.