Hukumar zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa tana shirin fito da sabbin tsare-tsare na zamani domin yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya ko sauya su ta hanyar fasahar AI, gabanin babban zaɓen 2027.

Hukumar ta bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara karo na 13, na ƙwararru kan fasahar Sadarwa ta Najeriya, ACSPN, mai taken “Kafofin Yaɗa Labarai, Fasaha da Zaɓe a Afirka: Fuskantar Sauye-sauyen Fasaha da Sabbin Hanyoyin Sadarwar Zaɓe.”

Da yake jawabi a madadin Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, Kwamishinan hukumar na kasa, Farfesa Sani Muhammad Adam, SAN, ya ce INEC ta fara shirye-shiryen zaɓen 2027, ciki har da duba cikakken tsarin fasahar zaɓenta, da gwajin tsaron tsarin kwamfuta, da samar da madadin tsarin aiki da kuma shirin dawo da bayanai idan wata matsala ta faru.

Ya ce hukumar, na nazarin yiwuwar gudanar da gwajin zaɓen shugaban ƙasa kafin ranar zaɓe, domin tabbatar da cewa tsarin fasahar zaɓen zai iya jure matsaloli da kuma matsin lamba da ka iya tasowa a lokacin zaɓe.

Farfesa Sani, ya ce darussan da aka koya daga zaɓen 2023 sun nuna cewa fasaha kaɗai ba za ta iya tabbatar da amincewar jama’a ba, duk da cewa tsarin BVAS da tashar IReV sun taimaka wajen ƙara bayyana gaskiya a tsarin zaɓe.

Hukumar ta ce za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da masana sadarwa, jami’o’i, kafafen yaɗa labarai, masu tantance gaskiyar bayanai, kamfanonin fasaha da ƙungiyoyin fararen hula domin samar da ingantaccen yanayin yaɗa bayanan zaɓe.

Shugaban ACSPN na ƙasa, Farfesa Rotimi Williams Olatunji, ya yi kira da a samar da tsarin haɗin gwiwa tsakanin INEC, jam’iyyun siyasa, kafafen yaɗa labarai, kamfanonin fasaha, ƙungiyoyin fararen hula da jami’o’i domin kare sahihancin bayanan zaɓe.

Darakta-Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya yi gargaɗin cewa bayanan ƙarya da AI ta samar ko kuma aka sauya ta hanyar fasahar zamani ka-iya rage amincewar jama’a da zaɓen 2027 idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.

Taron ya haɗa masana sadarwa, ‘yan jarida, masu tsara manufofi, jami’an gudanar da zaɓe da ƙwararru, inda suka tattauna barazanar da dama da sabbin fasahohi ke kawowa tsarin sadarwar zaɓe a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *