Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana cewa ba alhakinta ba ne kula ko hana yawon shanu a cikin Birnin Tarayya na Abuja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, CSP Ani Iniedu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin taron haɗin gwiwa kan tsaro, a lokacin da yake amsa tambayoyi game da damuwar da mazauna birnin ke nunawa kan yawon da shanu ke yi akan titunan Abuja.
A cewar Iniedu, nauyin sarrafa dabbobin ya rataya ne a wuyan hukumomin da ke kula da muhalli, amma yan sanda kan shiga cikin lamarin ne idan har dabbobin suna da hannu wajen aikata wani laifi.
“Nauyin sarrafa dabbobi yana ƙarƙashin Ma’aikatar ko Sashen da ke Kula da Muhalli ne, Inda mu muke shigowa shi ne idan saniya ta aikata laifi, ko kuma tana da sa hannu wajen lalata dukiyar ko shiga gonar wani ba tare da izini ba” Inji shi.
Ya ƙara da cewa rundunar zata gudanar da bincike nan take a kan duk wani korafi da aka shigar gabanta game da laifukan da ake zargin yawon dabbobin da aikatawa.
Wannan bayani ya biyo bayan ƙaruwar fargabar da al’umma ke nunawa kan yadda shanu ke yawo a manyan hanyoyi da sauran sassa na birnin Abuja, wanda ke haifar da cunkushewar ababen hawa, barazana ga tsaro da lalata dukiya.
A gefe guda kuma, Ministan Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya kaucewa bayani kan lamarin, inda ya bayyana cewa abu ne da ya shafi tsaron ƙasa.
“Ina da ikon magance matsalar kiwon shanu a Abuja, amma ba zan magantu a kansa ba saboda ya shafi tsaron ƙasa ne, wannan kuma sai dai aje wajen Mai baiwa Shugaban kasa shawara kan tsaro ko kuma Darakta Janar na Hukumar tsaro ta farin kaya DSS” Inji Wike