Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa da Masana’antu Cif Emeka Obegolu, ya ce za a gudanar da bikin baje kolin harkar noma na AGROMEQA Expo 2026 a Abuja tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Oktoba.

Obegolu ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, inda ya ce taken taron shi ne “Fasaha da Zuba Jari domin Fitar da Kayayyakin Noma zuwa Kasashen Waje.”

Obegolu, wanda Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Farko, Farfesa Adesoji Adesugba, ya wakilta, ya ce bikin zai mayar da hankali kan amfani da injina wajen noma, ƙara darajar amfanin gona da kuma ƙara shigar matasa cikin harkar noma.

Ya ce noma na da muhimmiyar rawa wajen sauya tattalin arzikin Najeriya, amma ana buƙatar sauya salon noma na gargajiya zuwa tsarin zamani.

Shugaban ACCI ya ce fannin noma na buƙatar ƙarin amfani da injina, sabbin dabaru, fasaha, zuba jari, bincike da kuma inganta hanyoyin haɗa manoma da kasuwanni.

Ya ce AGROMEQA Expo wani yunƙuri ne na haɗin gwiwa domin hanzarta zamanantar da harkar noma, wanda zai iya zama hanyar samar da ci gaban tattalin arziki da wadata ga ƙasa.

A cewarsa, ƙarin amfani da injinan noma da zuba jari mai tsari na iya buɗe damar da ke cikin fannin tare da samar da guraben ayyukan yi masu kyau ga ‘yan Najeriya.

Ya ƙara da cewa hakan zai ƙarfafa tattalin arzikin yankunan karkara, inganta samar da abinci da kuma ƙara darajar kayayyakin noma kafin a fitar da su zuwa kasuwannin cikin gida da na waje.

Bikin zai haɗa gwamnati, masu zuba jari a harkar noma, kamfanonin kera injinan noma, masu samar da fasaha, cibiyoyin bincike, ƙungiyoyin manoma, cibiyoyin kuɗi, masu sarrafa amfanin gona da masu fitar da kayayyakin noma zuwa ƙasashen waje.

Ana kuma sa ran halartar ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma.

Za a baje kolin injinan noma na zamani, kayan aikin noma daidaito, tsarin ban ruwa da fasahohin da suka dace da sauyin yanayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *