Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta amince da murabus ɗin tsohon Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) Alhaji Ibrahim Gusau da sauran mambobin kwamitin gudanarwarsa.

FIFA ta kuma yi alƙawarin ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Najeriya, da Hukumar NFF da kuma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) kan sababbin tsare-tsare da za su kawo gyara ga ƙwallon ƙafar Najeriya gaba ɗaya.

Wannan na ɗauke ne cikin sanarwar da daraktan yaɗa labarai na Hukumar NFF, Ademola Olajire, ya aike wa gidan rediyon Blueprint dake Abuja, a ranar Talata.

A cewar sanarwar, an cimma hakanne yayin wani taro da ya haɗa da jami’an Hukumar FIFA, da na CAF da kuma na Hukumar Wasanni ta Kasa (NSC) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Malam Shehu Dikko, yayin wani taro da ya wakana ranar Talata, a shelkwatar FIFA da ke Zurich, a ƙasar Switzerland.

Sanarwar ta ce an cimma matsayar ci gaba da tattaunawa domin kammala tsarin da zai tabbatar da aiwatar da gyare-gyaren da ake buƙata na ƙaramin lokaci, da kuma na dogon zango domin tafiya tare da kowa cikin yanayi mai kyau, da lumana da kwanciyar hankali wajen cimma nasara a ciki da wajen filin wasa domin ci gaban ƙwallon ƙafar Najeriya.

Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Malam Shehu Dikko ya ce “ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Hukumarsa, da jagorancin NFF da Hukumar CAF, da kuma na FIFA kan gyara harkokin ƙwallon ƙafar Najeriya gaba ɗaya.”

Dikko, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa daga ƙarshe, harkar ƙwallon ƙafar Najeriya zai kasance mai ƙarfi da tsari mai kyau bayan kammala wannan tsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *