Sojojin Operation HADIN KAI sun kwato ƙarin kayayyaki mallakar ’yan Boko Haram/ISWAP a yankin Alagarno na Jihar Borno, bayan wani hari da ’yan ta’addan suka kai wa sojoji a Kukawa ya ci tura.
A cikin wata sanarwa da mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar Kyaftin Mohammed Goni, na Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, ya fitar, ya ce an kwato kayayyakin ne a ranar 2 ga Satumba, 2026, yayin da sojoji ke ci gaba da gudanar da ayyukan bibiyar ’yan ta’addan a yankin Alagarno, da ke arewa maso gabashin Kukawa.
- Kamfanin Uber ya daina aiki a Najeriya
- Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda, sun kama albarusai masu yawa
- INEC na duba yiwuwar gudanar zaɓen shugaban ƙasa na gwaji kafin babban zaɓe
Sanarwar ta ce lamarin ya biyo bayan harin da ’yan Boko Haram/ISWAP suka kai wa sojoji a Kukawa a ranar 29 ga Agusta, 2026, wanda rundunar ta ce sojoji sun dakile.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai babura da barguna uku da wuƙa guda ɗaya da babbar tabarmar da kofuna da kayayyakin yin shayi da igiya da abin rufe kai da kuma wando mai ɗauke da tabon jini.
Kyaftin Goni ya ce gano tufafin da ke ɗauke da jini da sauran kayayyakin da ’yan ta’addan suka bari a baya na nuna cewa wasu daga cikinsu sun samu raunuka ko kuma sun rasa rayukansu yayin arangamar.
Ya ce sojojin na ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da share yankin domin hana ’yan ta’addan sake haɗuwa ko samun damar kai wani sabon hari.
Rundunar Operation HADIN KAI ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda lamba domin ƙarfafa nasarorin da aka samu da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.