Kamfanin sufuri na Uber, ya sanar da rufe ayyukan sa baki daya a Najeriya, tun daga ranar Laraba, 2 ga watan Satumbar shekarar 2026.
Mataimakin shugaban kamfanin Andrew Macdonald ne ya tabbatar da matakin, ta cikin wata sanarwa da ya aikewa abokan huldar sa.
Uber, ta bayyana cewa shawara ce mai wahala da ta yanke bayan gudanar da nazari mai zurfi kan harkokin kasuwancin su a kasar, amma ta mika godiya ga dukkan abokan huldar da aka kwashe shekaru 12 ana tare, tun farkon bude ayyukansu a birnin Lagos a shekarar 2014.
Har ila yau, Uber ta sanar da rage ma’aikata kusan 3,300 a daukacin rassan kamfanin na duniya, adadin da ya kai kaso 10 cikin dari.
Babban Darakta na Uber, Dara Khosrowshahi, ya bayyana cewa matakin zai shafi rage guraben ayyukan gudanarwa, don rage kashe kudade da sake tsarin gudanarwar su.
Khosrowshahi ya kara da cewa, ko da yake kamfanin na samun nasara a kasuwannin duniya, akwai buqatar rage nauyin tafikar da ma’aikata masu yawa domin fuskantar manyan ayyuka anan gaba.
Rage ma’aikatan shine mafi girma da kamfanin ya yi a baya-bayan nan, bayan irinsa da aka yi a bangaren hulda da jama’ar sa a tsakiyar shekarar nan.