A halin yanzu, ba abu ne mai ban mamaki ba cewa darajar dan wasa ta kai dalar Amurka miliyan 100, domin tuni dai lamarin ya zama kamar al’ada.
Gasar Firimiyar Ingila ta zama wajen nuna bajintar saya da kuma sayar da ‘yan wasa da kudade masu girman daraja.
Ga yadda kafar Sports Illustrated ta jera matsayin ‘yan wasa 22 da aka saya daga dala miliyan 100 zuwa sama a tarihin gasar.
- Antony — Daga Ajax zuwa Manchester United (Dala miliyan 100.2)

Wasu masu sharhi sun ce Antony shi ne mafi munin dan wasan da aka saya da tsada a tarihin Gasar Firimiyar Ingila.
Dan kasar Brazil, Antony, an saye shi ne da daraja sakamakon ya buga kaka biyu masu kyau da Ajax, hakan ya sa Man United ta kashe dala miliyan 100.2 a farkon zuwan koci Erik ten Hag.
Tabbas Ten Hag ya san shi da kyau, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba domin dan wasan bai tabuka abun azo a gani ba a United.
- Romelu Lukaku — Daga Inter Milan zuwa Chelsea (Dala miliyan135)

Wannan ya kamata ya zama babban sako daga zakaran Turai, wadda ta so ta mamaye kwallon Ingila karkashin koci Thomas Tuchel.
Amma maimakon haka, sai aka samu rashin jituwa tsakanin Lukaku da Tuchel, yayin kuma dan wasan na kasar Belgium, ya zargi Tuchel da rashin amfani da shi a wata hira da Sky Italia.
Lukaku ya koma Inter a matsayin dan wasan aro bayan kaka daya kacal.
Ya zura kwallaye 8 ne kacal a wasanni 26 na Firimiyar Ingila.
- Sandro Tonali — Daga Newcastle zuwa Spurs (Dala miliyan 133)

Dan kasar Italiyan ya yi matukar kyau tare da Newcastle a 2024-25 amma ya ji rauni a bara.
Sai dai ana ganin dan wasan tsakiyar darajarsa bata kai dala miliyan 133, amma hakan ba ya nufin ba shi da kyau ba ne.
- Alexander Isak — Daga Newcastle zuwa Liverpool (Dala miliyan 170)

Liverpool ta kashe kudi dala miliyan 170 kafin ta same shi a watan Satumbar 2025, sai dai babu wanda ya yi mamaki saboda Isak ya cancanci hakan.
Amma magoya bayan Reds suna tambayar ko za su taba ganin irin Isak din da suke tunanin sun saya.
Sai dai Isak ya zura kwallaye biyu da suka bai wa sabon kocin Liverpool, Iraola, nasarar shi na farko a kakar bana ta 2026/27 yayin karawa da Ipswich Town.
- Florian Wirtz — Daga Bayer Leverkusen zuwa Liverpool (Dala miliyan 133)

Wirtz ya yi kaurin suna ne sakamakon kakar wasan Bundesliga na 2023-24, inda Leverkusen ta lashe gasar ba tare da shan kaye ba. Zai iya zuwa Bayern Munich amma ya zabi zuwa Ingila.
A Kaka ta farko, ya bayar da gudunmawar kwallo 17 a wasanni 49 da ya buga.
- Sávio — Daga Man City zuwa Tottenham (Dala miliyan 115)

Kaka ta farko ta Sávio ta yi kyau, amma har yanzu magoya bayan kungiyar suna bukatar ya kara kokari.
- Kai Havertz — Daga Bayer Leverkusen zuwa Chelsea (Dala miliya 115.5)

Havertz ya zura kwallaye 32 kuma ya bayar da taimako 16 a wasanni 139 da ya buga wa Chelsea.
Magoya bayan Chelsea ba su yadda cewa Arsenal za ta saye shi akan kudi dala miliyan 86 a 2023 ba.
Chelsea ta yi asara a kasuwar dan wasan, amma sun yi farin ciki da suka rabu da shi.
- Ayyoub Bouaddi — Daga Lille zuwa Man City (Dala miliyan 115)

Akwai abun sha’awa game da Bouaddi, wanda matashin dan wasa ne mai hankali, inda zai maye gurbin Rodri a Man City.
Yana da shekaru 18 kacal kuma ya nuna kansa a Gasar Cin Kofin Duniya, sai dai watakila zai iya daukar lokaci kafin a ga tasirinsa a cikin fili.
- Mateus Fernandes — Daga West Ham zuwa Spurs (Dala miliyan 112)

Ko da yake ya samu koma baya sau biyu tare da Southampton da West Ham bayan sun fada gurbin gajiyayyu, amma har yanzu dan wasa ne mai dimbin baiwa.
Yana da kwarewar rike kwallo a kafarsa kuma yana iya kwato kwallo a kafar abokin karawa.
Zai iya zama mafi kyawun dan wasan da Spurs ta saya na bazarar 2026.
- Jack Grealish — Daga Aston Villa zuwa Man City (Dala miliyan 139)

Grealish ya sha suka sosai a City, amma rawar da ya taka a kakar da suka lashe kofuna uku ba za a ta ba manta da ita ba.
Ya buga wasanni 50.
- Paul Pogba — Daga Juventus zuwa Man Utd (Dala miliyan 116)

Magoya baya sun yi murna sosai da dawowar Pogba a 2016, inda ya nuna kwarewarsa a lokuta da dama, amma sai dai ya sha suka mara misaltuwa akan rashin jagorantar United zuwa lashe ko da kofi guda daya.
- Morgan Rogers — Daga Aston Villa zuwa Chelsea (Dala miliyan 157)

Rogers ya cancanci kudin da aka saye shi sakamakon bayar da gudunmawar kwallo 60 a wasanni 129 da ya buga wa Villa.
Sai dai fa, dala miliyan 157 kudi ne mai yawa.
Magoya bayan Chelsea na sa ran zai yi abubuwa da yawa tare da Cole Palmer karkashin jagorancin Xabi Alonso.
- Hugo Ekitike — Daga Eintracht Frankfurt zuwa Liverpool (Dala miliyan 106.1)

Dan wasan gaban ya na da kyau da kuma fasaha sai dai ya samu rauni, yayin da ake fatan zai dawo da karfinsa bayan ya warke daga jinya mai tsawo da ya tafi.
- Elliot Anderson — Daga Nottingham Forest zuwa Man City (Dala miliyan 155)

Dan wasa mai cike da fasaha, sai dai shin, ya cancanci zama na hudu mafi tsada a duniya?
Koci Enzo Maresca ne zai tabbatar da hakan.
- Harry Maguire — Daga Leicester zuwa Man Utd (Dala miliyan 108)

Shine mafi tsadar dan wasan baya a duniya, yayin da aka saka tsammani sosai akansa.
Sannan kuma, ya sha suka sosai daga wajen magoya baya.
A karshe, sayen na sa ya taimaka sosai yayin da United ta samu nasarar lashe kofuna 2 daga wasanni 273 da ya buga.
- Enzo Fernández — Benfica zuwa Chelsea ($131 miliyan)

Ya zo a lokacin da Chelsea ke cikin rudani, sai dai zuwan koci Maresca a 2024-25 ke da wuya, Fernández ya fara nuna bajintarsa.
Ya zura kwallaye 16 a kaka biyu na karshe, amma magoya baya ba su nuna damuwa ba lokacin da City ta saye shi.
- Enzo Fernández — Daga Chelsea zuwa Man City (Dala miliyan 168)

Dan wasa ne mai kyau. Chelsea ta ci riba sosai akan City.
Yanzu dai, ya koma karkashin kocin da ya ba shi damar nuna fasaharsa wato, Maresca.
Shin kwalliya za ta biya kudin sabulu kuwa?
- Bradley Barcola — Daga PSG zuwa Liverpool (Dala miliyan 166)

Yayin da wasu suna ganin kamar kudin da aka sayi dan wasan ya yi yawa, sai dai fa kwarewarsa da kuma kokarinsa ya cancanci hakan.
Gaskiya ne, ba shi da inganci sosai wajen zura kwallo amma yana da hadarin gaske a koyaushe.
Ya taimaka wa PSG wajen lashe Gasar Nahiyar Zakarun Turai sau biyu a jere.
- Joško Gvardiol — Daga RB Leipzig zuwa Man City (Dala miliyan 104)

Dan wasan baya na biyu mafi tsada a tarihi.
Tun 2023, ba a yi amfani da shi a wajen da aka saye shi ba, sai dai an fi amfani da shi a gaba.
Yana bayar da gudunmawar cin kwallo a kowane wasanni 5 kuma yana iya kare gida idan bukatar haka ya taso.
- Moisés Caicedo — Daga Brighton zuwa Chelsea (Dala miliyan 146)

Idan aka manta da rashin kokarinsa na wasan farko. Tun 2023 Caicedo ya kasance ginshiki a Chelsea. Ba ya samun hutawa, duk sabon kocin da ya zo kungiyar, ya na dogaro da shi. Shi ne wanda ke daidaita tawagar.
- Bruno Guimarães — Daga Newcastle zuwa Arsenal (Dala miliyan 101)

Arsenal ta yi imanin ta samu tabbataccen dan wasa mai inganci.
Ya bai wa Gunners wahala a 2022 yayin da Newscastle ta lallasa Arsenal da ci 2-0, ta janyo mata rashin zuwa Gasar Zakarun Turai a wannan lokacin.
Ana sa ran zai taimaka wa Arsenal sosai yayin buga manyan wasanni.
- Declan Rice — Daga West Ham zuwa Arsenal (Dala miliyan 137.5)

Yawancin ‘yan wasan da aka saya da tsada na dala miliyan 100 zuwa sama ba su yi tasiri ba.
Da yawansu hayaniya ce kawai.
Amma Rice ya kasance na daban, ya zama abun alfahari ga Gunners.
A koyaushe, yana nan kuma yana bayar da gudunmawarsa.
Rice ya kasance daya daga cikin ’yan wasan tsakiya mafi kyawun gaske a duniya tun da ya zo Arsenal.
Kuma haka ake son aga dan wasa ya nuna cancantar darajar dala miliyan 100 da aka sayesa.
