Shelkwatar ‘Yan Sandan Najeriya (NPF) ta sanar da samun gagarumar nasara a ayyukan tsaro da ta gudanar a jihohi da dama da kuma yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A cikin nasarorin da ta samu da akwai kashe ‘yan fashi ɗauke da makami guda biyu, da ceto wani da aka yi garkuwa da shi, da kuma kama wasu mutane da dama da ake zargi da aikata laifuka irin su garkuwa da mutane, da ta’addanci, da ɓarnata kayan gwamnati, da fashi da makami da kuma laifukan miyagun ƙwayoyi.
Acewar Shelkwatar ta ’yan sanda, an gudanar da ayyukan ne tsakanin ranar 2 zuwa 5 ga watan Satumba.
-
Soji sun kashe ɗan ta’adda, sun kwato babura huɗu a Katsina
-
‘Yan sanda sun kama miyagun ƙwayoyi a Delta
-
Rundunar soji na hada gwiwa da masu zaman kansu don kiwon Lafiyar Sojoji
Sannan kuma, ta ce ta ƙwato makamai da harsasai da babura da aka sata da miyagun ƙwayoyi da bututun Kamfanin man fetur na Kasa NNPCL da aka lalata da kuma sauran kayan da aka kama.
Jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, CSP Ani Iniedu ne ya sanya hannu kuma ya fitar da taƙaitaccen rahoton ayyukan daga shelkwatar, inda ya ce kame da kuma kwato kayayyakin sun nuna kokarin ‘yan sanda na ci gaba da yaki da laifuka a fadin kasar.
Sanarwar ta ce a Jihar Nasarawa, ‘yan sanda sun kashe ‘yan fashi ɗauke da makami guda biyu bayan musayar wuta da suka yi da jami’ai, bayan sun yi fashi a Kauyen Uluji da ke Ƙaramar Hukumar Keana.
A yankin Birnin Tarayya Abuja, ‘yan sanda sun kama wani matashi mai shekaru 27 de ake zargin aikata laifin fashi da makami da kuma fyaɗe a yankin Pegi.
‘Yan sandan sun ce wanda ake zargin yana taimaka musu da bayanai da zasu kai ga kama sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.
Har ila yau, a yankin na Abuja, ‘yan sanda sun kama mutane 4, yayin wani sintiri da aka yi a kusa da Masallacin Ƙasa kan zargin lalata fitillun haskaka kan titi dake amfani da hasken rana.
Sannan kuma sun ƙwato fitillun da aka lalata da sandar su a matsayin hujja.