Fadar shugaban Najeriya ta yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa game da wata shari’a da ke gudana a Amurka a ƙarƙashin dokar neman bayanan gwamnati, inda ta ce matsala ta ƙananan laifuka, ba shari’ar aikata babban laifi ba ne da ake yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, fadar shugaban ƙasa ta ce shari’ar da ke gaban kotun tarayya ta Amurka da ke Gundumar Washington, D.C., ta haifar da wasu fassarori da ba daidai ba game da Shugaba Tinubu da kuma ainihin abin da shari’ar ta ƙunsa.

Shari’ar ta shafi bukatar samun wasu bayanan gwamnatin Amurka da suka shafi Mista Tinubu, da kuma ko wasu daga cikin takardun da hukumomin Amurka ke riƙe da su za a iya bayyana su ga jama’a.

Wannan dai ya biyo bayan sukar da fadar shugaban Njeriyan ke ci gaba da fuskanta, musamman daga ƴan adawa masu neman a fitar da dukkan bayanan shari’ar da shugaban Najeriya ya taɓa fuskanta a 1990, inda suke zargin akwai ɗimbin sirri da za a iya bankaɗowa a ciki.

Fadar shugaban ƙasar ta ce kotun ba ta taɓa samun Shugaba Tinubu da aikata wani laifi ba.

Me shari’ar ta ƙunsa?

Shari’ar ta fara ne bayan da Aaron Greenspan ya gabatar da buƙatar samun bayanai a shekarar 2022 a ƙarƙashin dokar ƴancin samun bayanai ta Freedom of Information Act (FOIA) ta Amurka.

Ya nemi hukumomin gwamnatin Amurka daban-daban su ba shi bayanan da suka shafi Shugaba Tinubu.

Bayan wasu hukumomin sun ƙi sakin wasu bayanai ko kuma suka ƙi tabbatarwa ko musanta kasancewar wasu bayanai, Mista Greenspan ya shigar da ƙara mai lamba Civil Action No. 23-1816 a kotun tarayya ta Amurka da ke Gundumar Washington, D.C., a shekarar 2023.

Daga baya kotun ta ba Shugaba Tinubu damar shiga cikin shari’ar a matsayin mai shiga tsakani (intervenor).

Fadar shugaban Najeriya ta bayyana wata wasiƙa mai kwanan wata 4 ga Fabrairun 2003, wadda Ofishin Jakadancin Amurka da ke Legas ya aika wa tsohon Sufeto-Janar na ƴansandan Najeriya, Tafa Balogun.

A cewar fadar gwamnatin Najeriya, wasiƙar ta bayyana cewa wani binciken bayanan da FBI ta gudanar bai gano tarihin kama Tinubu da laifi ba, ko kuma wata takardar nemansa ko kuma umarnin kama shi. Wannan ya faru ne a lokacin da Tinubu yake gwamnan Jihar Legas.

Gwamnatin Najeriya ta sake buga misali da wasiƙar a bayanin da take yi kan shari’ar neman bayanan, musamman a yanzu ɗin ana nema bayanan shugaban ƙasar ne.

Me ya sa hukumomin Amurka suka ɓoye wasu bayanai?

A yayin shari’ar, wasu hukumomin gwamnatin Amurka sun yi amfani da abin da ake kira “Glomar response”.

Wannan wata hanya ce da hukumomin Amurka za su iya amfani da ita a wasu yanayi, domin ƙin tabbatarwa ko musanta tabbatar da masaniya game wasu bayanai ko bincike da suke yi.

Ana iya amfani da wannan mataki idan bayyanawa ko musanta kasancewar bayanan zai iya tona asirin wasu ayyukan jami’an tsaron ƙasar ko tsare-tsaren bincike ko bayanan sirri ko kuma sunayen masu bayar da bayanai.

Daga baya kotun ta amince da buƙatar CIA, da ofishin babban mai shari’a na ƙasar da da ma’aikatar harkokin wajen Amurka da ma’aikatar baitulmali da kuma hukumar haraji ta Amurka (IRS), inda aka cire su daga shari’ar.

Sai dai ɓangarorin shari’ar da suka shafi FBI da hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Amurka (DEA) sun ci gaba da kasancewa a gaban kotu.

FBI da DEA sun fitar da shafuka 399

A cewar fadar shugaban Najeriya, daga bisani FBI da DEA sun fitar da shafi 399 na takardu, amma an ɓoye wasu bayanan.

Sai dai mai shigar da ƙarar ya ƙalubalanci wannan mataki, inda ya nemi a sake bayyana ƙarin bayanan da aka ɓoye.

Sai dai FBI da DEA, ta hannun ma’aikatar shari’a ta Amurka, sun ƙalubalanci buƙatar, suna masu cewa wasu bayanan doka ta kare su daga bayyana wa jama’a.

Sanarwar fadar gwamnatin Najeriya ta ce daga cikin dalilan da hukumomin suka bayar akwai kariyar bayanan da suka shafi zaman Grand Jury, wasu bayanan da suka shafi hanyoyin sa ido, bayanan da ke ƙarƙashin kariyar lauya da wanda yake wakilta, bayanan sirri na mutane, masu bayar da bayanan sirri da kuma dabarun da hukumomin tsaro ke amfani da su wajen binciken laifuka.

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan shawarar lauyoyi ne Tinubu ya kuma nemi kariyar bayanan sirri da aka tanada a ƙarƙashin FOIA Exemption 7(C).

Me ya sa batun ya sake kunno kai yanzu?

Shari’ar ta fara ne tun shekarar 2023, amma ta sake ɗaukar hankalin jama’a ne sakamakon sabbin abubuwan da suka faru a shari’ar da kuma sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar domin ƙarin bayani.

A bisa bayanin fadar shugaban ƙasa, wannan ba shari’ar aikata manyan laifuka ba ce, inda ta nanata cewa ba a kama shugaban ƙasar da wani laifi ba.

Amma a gefe guda wasu ƴan ƙasar suna bayyana shakkunsu kan ƙarar da gwamnatin ta shigar domin hana fitar da bayanan baki ɗaya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar babban zaɓen ƙasar na shekarar 2027, inda Bola Tinubu ke neman zarcewa domin zuwa wa’adi na biyu, yayin da a gefe guda kuma jam’iyyun hamayya suke ta ƙoƙarin kayar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *