Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai wa manema labarai da ke ɗauko rahoton taron jam’iyyar All Progressives Congress (APC) hari a Jihar Kano ranar Asabar.
An kai musu harin ne a bayan harabar City Campus ta Jami’ar North West, Kofar Nassarawa, sa’ilin da suke kan hanyarsu ta komawa ofis bayan kammala taron.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun fasa motar hukuma ta gidan rediyon Rediyon Nijeriya (Radio Nigeria) da ke ɗauke da manema labaran sannan suka lalata gilashin bayanta.
Jariidar Daily Trust ta ruwaito cewa da farko jam’iyyar ta ƙaddamar da taron ƙungiyar goyon bayan Tinubu (Tinubu Support Group) a filin wasa na Sani Abacha Stadium da ke Kano, sannan kuma ta karɓi wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka sauya sheƙa.
- Gwamnatin Plato ta bada umurnin rufe makarantu saboda cutar diphtheria
- Za a haɗe wasu makarantun sakandiren kwana saboda karancin Ɗalibai – Gwamnatin Katsina
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ɗaya daga cikin manema labaran da ke aiki da gidan rediyon Pyramid Radio a Kano, Yakubu Abubakar Gwagwarwa, ya ce motar tana ɗauke da manema labarai guda biyar da jami’an ‘yan sanda guda uku lokacin da aka kai musu harin.
Ya ce ‘yan daban sun ɗauki adduna da wuƙaƙe, inda suka riƙa fasa tagogin motar akai-akai tare da lalata wasu sassa na motar bus ɗin
Gwagwarwa ya ce, “A cikin motar akwai ma’aikatan Rediyon Nijeriya Pyramid FM guda huɗu, ɗan jarida ɗaya na Guarantee Radio da kuma jami’an ‘yan sanda guda uku da muka rage musu hanya daga filin wasa na stadium.
“Amma ko kasancewar jami’an tsaron a cikin motar bai hana maharan aiwatar da harin ba. “Sun ci gaba da dukan motar duk da cewa akwai jami’an tsaro da manema labarai a ciki. Dole ta sa muka juya da sauri, amma duk da haka suka biyo mu,” in ji shi.
Ɗan jaridar ya ce sakamakon haka, direbansu ya ji rauni kuma wasu daga cikinsu sun sami raunuka daga gutsuren gilasan motar da aka fasa.
To sai dai kuma, ya ce harin mai yiwuwa ba su aka nufa da shi kai-tsaye ba, inda ya bayyana shi a matsayin harin kwatsam ga duk wanda aka haɗu da shi, yana mai ƙarawa da cewa wasu ma za a iya kai musu harin.
Wannan ba shi ne karon farko da ‘yan dabar siyasa ke kai wa mutane hari a jihar yayin harkokin siyasa ba. Watanni kalilan da suka gabata, aƙalla mutane uku aka ruwaito sun mutu sakamakon harin da ake zargin ‘yan dabar siyasa ne suka kai a ranar rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan jihar.