Shugaban Majalisar Wakilai ta Kasa, Honarabul Tajudeen Abbas, ya ba da umarnin rushe dukkan kwamitocin wucin gadi na majalisar tare da tsayar da dukkan ayyukan su.

Umarnin rushewar ya fito ne ta cikin wata sanarwa da Sakataren Majalisar Malam Sidi Ibrahim, ya fitar a ranar Asabar, 5 ga Satumbar, 2026, zuwa ga shugabanni da mambobin kwamitocin.

Sanarwar ta bayyana cewa, daukar matakin ya biyo bayan kiran da aka yi wa kwamitocin tun a baya, da su kammala ayyukan da aka dora musu tare da mika rahotanninsu kafin cikar wa’adi.

Sakataren yace kwamitoci biyu ne kacal suka nemi karin wa’adi, inda aka kara musu tsawon makonni biyu, wanda a yanzu shi ma wa’adin ya kare.

“Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya umarce ni da in sanar da dukkan mambobi cewa an rushe dukkan kwamitocin wucin gadi na majalisa nan take,” in ji sanarwar.

Sakataren ya kuma tunatar da mambobin majalisar cewa, tsarin doka ya gindaya kwamitocin wucin gadi gudanar da wasu nauye-nauye da majalisa ta dora musu na wani kayyadadden lokaci, bawai an kafa su ne dindindin ba.

Bisa la’akari da doka ta 18, sashe na 11, sakin layi na 5 na ka’idojin aikin Majalisar, an kayyade wa’adi da kowanne kwamiti zai mika rahotan sa, wannan ke tabbatar da cewar Majalisa kan nada kwamiti a matakin wucin gadi domin aiwatar da wani aiki mai muhummanci bisa ka’ida.

Tun daga ranar Juma’a, 28 ga Agustan shekarar 2026 ne wa’adin kwamitocin ya cika, wanda ke kawo karshen dukkan ayyukan da suke gudanarwa a ko’ina.

An kuma umarci shugabannin kwamitocin da abin ya shafa da su mika dukkan rahotanni da ba su kammala ba, takardun aiki, da ma sauran bayanai zuwa ofishin Sakataren Majalisar Wakilai domin adanawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *