Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da kuma Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta (NDLEA) sun cafke tankar mai da ake amfani da ita wajen safarar hodar ibilis mai nauyin kilo 2,145.
An cafke tankar man mai lamba MKA 960 XC a kan Titin Akoko/Lokoja a Jihar Ondo a ranar Juma’a, 4 ga Satumba, 2026, yayin da direbanta ya ƙi tsayawa bayan jami’an NDLEA sun buƙaci da ya tsaya.
A cewar Daraktan Yaɗa Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, direban ya bar tankar a harabar wata coci a Ugbe Akoko sannan ya gudu ya shiga daji, hakan ya sanya jami’an suka gudanar da bincike cikin tankar.
-
‘Yan sanda sun kashe ‘yan fashi tare da cafke wasu da dama
-
Abubuwa biyu da za su iya tantance wanda zai lashen zaɓen Najeriya na 2027
-
Datti Baba-Ahmed: Babu ɗaya daga manyan masu ƙalubalantar Tinubu da zai iya inganta Najeriya
Binciken na su ya gano wani ɓoyayyen wuri a cikin tankar, inda aka samu buhu 165 na hodar ibilis masu nauyin kilo 2,145 gaba ɗaya, tare da man fetur na asali da ake zargin an tura zuwa garin Jos, a Jihar Filato.
A cewar NDLEA, tankar ta daɗe tana tserewa a saboda haka cafke ta nasara ce mai girma a ƙoƙarin hukumar na amfani da bayanan sirri wajen murƙushe hanyoyin safarar miyagun ƙwayoyi isa ga jama’a.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami’an da suka gudanar da ayyukan, inda ya buƙace su da su ci gaba da jajircewa wajen amfani da tsarin hukumar na yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
Marwa ya jaddada cewa duk masu safarar ƙwayoyi da ke ƙoƙarin ɓoye kansu da sababbin sunaye, kamfanoni na halal, ko hanyoyin ɓoye na zamani, hukumar za ta ci gaba da binsu har ta cafke su.
