Aƙalla mutane 25 ne suka mutu sakamakon wani hatsarin motar bas a ƙasar Cape Verde, mafi yawan wadanda abin ya rutsa da su yara ne da matasa, kamar yadda gidan rediyon ƙasar RCV ya ruwaito a ranar Lahadi.

Hukumomin yankin tsibirin Fogo, inda hatsarin ya faru, sun ce wasu mutane da dama sun samu raunuka, ciki har da waɗanda raunukansu suka yi tsanani.

Hatsarin ya faru ne ranar Asabar lokacin da bas ɗin ke dawo wa zuwa Sao Filipe daga wani yawon buɗe ido zuwa kogon dutsen mai aman wuta na Pico do Fogo.

Bas ɗin ta kauce daga hanya sannan ta faɗa cikin wani kwazazzabo mai zurfi. Mutane 32 ne ke cikin bas ɗin a lokacin hatsarin.

Direban bas ɗin na daga cikin waɗanda suka mutu.

Kuma shi ne ke shirya wannan yawon buɗe ido zuwa wannan wuri na musamman a kowace shekara a matsayin kyauta ga ɗaliban da yake kaiwa makaranta a lokacin karatu.

Shugaban ƙasar Cape Verde, José Maria Pereira Neves, ya bayyana hatsarin a matsayin “babbar masifa” a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *