Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai shekaru 35, bisa zarginsa da sojan gona na muƙamin babban jami’in ‘yan sanda na CSP kuma ke amfani da hotunan da AI ta samar domin yaudarar masu neman aiki.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, na Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na sa da zumunta.
A cewar rundunar, an kama shi ne sakamon bayanan sirri da aka samu da misalin karfe 7:30 na dare a ranar 1 ga Satumba, 2026, daga offishin ‘yan sanda da ke Challawa, Kano.
-
Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin biyan Lakcarori alawus din ‘CATA’
-
’Yan sandan FCT sun kama matar da ake zargi da zuba wa makwabciyarta ruwan zafi
-
NDLEA ta cafke wani da ake zargi da safarar hodar Iblis mai nauyin kilogiram 49.70
A cewar sanarwar, bayanan sirrin sun taimakawa ‘yan sanda na ofishin Panshekara kama wanda ake zargi, mazaunin unguwar Kureken Sani, a Kano.

Sanarwar ta ƙara da cewa, bincike ya nuna wanda ake zargin ya ƙware wajen karɓar kuɗi daga mutane ta hanyar cewa yana da tasiri a kan sama musu guraben aiki da kuma canja wuraren aiki a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Rundunar ’yan sandan ta ce wanda ake zargin ya na amfani da ƙirƙirarriyar fasaha ta AI wajen haɗa hotuna na ƙarya inda aka nuna shi tare da manyan jami’an ‘yan sanda.
“Ya na amfani da waɗannan hotuna na ƙ arya, tare da sunayen manyan jami’ai, domin yaudara da kuma damfarar mutane cewa zai iya sama musu guraben aiki da canja musu wurin aiki,” in ji CSP Kiyawa
Bayan gudanar da bincike a gidan wanda ake zargin, an samu abubuwa da suka haɗa da kayan sarki da baƙaƙen takalma guda 2 da kuma tsabar kuɗi Naira 300,000 da sauransu.
Kakakin ‘yan sandan ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.