Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta sanar da cafke wani da take zargi da jagorantar safarar miyagun ƙwayoyi, bayan ya kwashe sama da shekaru biyu yana gudun kamun hukuma.
NDLEA ta ce wanda ake zargin na daga cikin mutane uku da aka ayyana a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo, bayan jami’an hukumar sun kama kilogiram 49.70 na hodar Iblis a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas a watan Fabrairun 2024.
An ɓoye kayan cikin kwalayen injinan yanke ƙarfe.
Binciken ya kuma kai ga rufe asusun banki 107 da kuma kwace wasu ƙadarorin da ake dangantawa da ƙungiyar.
A cewar hukumar, wanda ake zargin ya koma Mozambique, inda yake gudanar da harkar otal a matsayin wata hanya ta ɓoye ayyukansa.
- INEC ta hada kai da bangaren tsaro domin tabbatar da bin dokokin kamfen
- An fara kamfe na zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi
- An fara kamfe na zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi
Ya kuma riƙa shiga da fita tsakanin Mozambique da Najeriya ta Jamhuriyar Benin domin guje wa jami’an tsaro.
Sai dai bayan samun bayanan sirri, an cafke shi a filin jirgin sama na Cotonou, daka ƙasar Benin, ranar 2 ga Satumba 2026, kafin a miƙa shi ga jami’an NDLEA a ranar 4 ga Satumba.
Hukumar ta ce wanda ake zargin, mai shekaru 52, ya tabbatar da asalinsa a yayin bincike, tare da bayyana cewa ya sauya suna, a ranar 5 ga Satumba, an kai shi wajen ajiyar kayan shaida na NDLEA a Ikoyi, Legas, inda ya gane kwalayen hodar Iblis ɗin da ke ɗauke da lambar “ND” da aka danganta da shi.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya bayyana cafke wanda ake zargi a matsayin gagarumar nasara wajen farautar masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka gudu.
Ya ce dogon hannun hukumar zai kai ga duk wanda ke da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi, ko da kuwa ya gudu daga Najeriya ko ya ɗauki tsawon lokaci yana ɓoye.