Shugaban Gambia, Adama Barrow, ya yi alkawarin ƙara samar da wutar lantarki a ƙasar nan da ƙarshen watan Oktoban 2026, bayan zanga-zangar da ta ɓarke sakamakon yawan katsewar wuta da ƙasar ke fama da shi tun watan Yuni.
An shafe makonni ana samun matsalar wutar lantarki, inda a wasu yankunan ake iya ɗaukar tsawon sa’o’i 48 babu wuta.
Lamarin ya fi tsanani ne a lokacin zafi, lamarin dake ƙara wahalar da rayuwar al’ummar ƙasar.
A daren Litinin zuwa Talata ne masu zanga-zanga a babban birnin Banjul da wasu garuruwan dake kusa suka fito kan tituna, inda suka kona abubuwa tare da tare hanyoyin mota.
Wasu daga cikinsu na rera taken neman Shugaba Barrow ya sauka daga mulki.
A yankin Westfield kuma, ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka nufi hedikwatar kamfanin samar da wutar lantarki da ruwa na NAWEC.
Shugaba Barrow ya bayyana matsalar wutar lantarkin a matsayin “lamarin tsaron ƙasa” da kuma “gaggawa”.
-
Iran da Amurka sun tsananta musayar hare-hare a tsakanin su, yayin da rikicin mashigar Hormuz ke kara tsananta.
-
NFF ta naɗa Eguavoen kocin wucin gadi na Super Falcons
-
An fara kamfe na zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi
Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta ɗauki matakin magance matsalar, yayin da ya ziyarci tashar samar da wutar lantarki ta NAWEC da ke Brikama, kusa da babban birnin ƙasar.
Ya ce gwamnati na shirin kammala girka wata sabuwar injin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 24 zuwa ƙarshen Oktoba.
A cewarsa, wannan ƙarin wutar zai iya kawo gagarumin sauyi wajen samar da wutar lantarki ga gidajen al’umma.
Ya kuma ce an riga an bayar da kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana mai ƙarfin megawatt 50 a Soma.
Hukumar NAWEC ta ce yawan buƙatar wutar lantarki, musamman saboda tsananin zafi, da kuma matsalolin shigo da wutar lantarki daga wasu wurare ne daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalar.
Manajan daraktan hukumar, Gallo Saidy, ya kuma danganta matsalar da sauyin yanayi da kuma tasirin yaƙe-yaƙe a Gabas ta Tsakiya, tare da neman jama’ar Gambia su yi haƙuri.
Zanga-zangar ta zo ne ‘yan watanni kafin zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Disamba, wanda Shugaba Barrow ke neman wa’adinsa na uku.
Ministan Yaɗa Labarai, Ismaila Ceesay, ya ce gwamnati na ɗaukar matsalar da matuƙar muhimmanci da gaggawa, tare da yin aiki ba dare ba rana domin inganta samar da wutar lantarki a ƙasar.