Tsohon kocin Super Eagles Augustine Eguavoen zai jagoranci tawagar ’yan matan Najeriya ta Super Falcons, na wucin gadi a wasannin neman tikitin shiga Gasar Olympics ta 2028 da za ta buga da Comoros a watan Oktoba, yayin da ake ci gaba da neman kocin dindindin na tawagar.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF, ce ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaranta, Ademola Olajire, ya aike wa Gidan Rediyon Blueprint dake Abuja a daren ranar Talata.
Sannan kuma NFF ta ce koci Christopher Danjuma, na ƙungiyar Nasarawa Amazons, shi ne zai taimaka masa, yayin da tsohon mai horas da masu tsaron ragar Super Eagles, Olatunji Baruwa, zai riƙe muƙamin mai horar da masu tsaron raga.
-
Najeriya za ta kara da Russia a wasan sada zumunta
-
An fitar da sunayen ‘yan takarar kyautar Ballon d’Or ta 2026
-
FIFA ta dakatar da zeɓen NFF
Har ila yau, tsohuwar ‘yar wasan baya ta Super Falcons kuma yanzu koci, Ayisat Yusuf, za ta riƙe muƙamin mai taimakawa ɗaya daga cikin masu horas da ‘yan wasan.
Falcons, wadda ta lashe Gasar Nahiyar Afirka ta Mata har sau 10, za ta fara buga wasan neman tikitin Olympics a zagaye na biyu da Comoros, inda aka tsara za a buga wasanni biyu a filin wasa na Remo Stars da ke Ikenne a ranar 9 da 13 ga Oktobar 2026.
Idan Super Falcons ta yi nasarar doke Comoros, za ta tsallaka zuwa zagaye na 3 da aka tsara za a buga tsakanin ranar 23 ga Fabrairu zuwa 6 ga Maris 2027, inda za ta kara da ɗaya daga cikin ƙasashen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ko kuma Morokko.
Idan ta samu shiga zagaye na 4, Najeriya za ta fuskanci ɗaya daga cikin ƙasashen Tunisia ko Senegal ko Benin Republic ko Mali, tsakanin 4 zuwa 12 ga Oktoba 2027.
Zagaye na ƙarshe na wasn neman tikitin an tsara za a buga daga ranar 23 ga Nuwamba zuwa 4 ga Disambar 2027, inda Falcons za ta iya fuskantar ɗaya daga cikin ƙasashen Guinea ko Cameroon ko Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ko Côte d’Ivoire ko Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ko Aljeriya ko kuma Burkina Faso.