Tambarin FIFA da na NFF

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, ta bayyana cewa ba ta cimma matsayar ƙarshe ba kan matsalar shugabancin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF).

FIFA ta ce har yanzu tana nazarin abubuwan da suka haddasa murabus ɗin tsohon Shugaban NFF, Alhaji Ibrahim Gusau, da Babban Sakatare Mohammed Sanusi, da kuma mambobin Kwamitin Zartarwa na NFF.

Murabus ɗin na su, yana da nasaba da ƙorafe ƙorafen al’umma sakamakon koma baya da manyan tawagun ƙwallon ƙafa na ƙasar suka samu na rashin samun tikitin shiga Gasar Cin Ƙwallon Ƙafa na Duniya da kuma rashin taɓuka abun kirki a gasar nahiya da kuma na ƙasa da ƙasa..

Cikin sanarwar da FIFA ta fitar ranar Litinin, 7 ga watan Satumbar 2026 ɗauke da sanya hannun Elkhan Mammadov, FIFA ta ce jami’anta da kuma Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nahiyar Afirka za su ziyarci Najeriya don gudanar da cikakken bincike.

“FIFA da CAF, suna rokon da a dakatar da tsare-tsaren zaɓen da ake son a gudanar, sannan kada a ɗauki wani mataki ko yanke wani hukunci game da wannan al’amari har sai abinda hali ya yi,” in ji sanarwar.

FIFA ta bayyana cewa har yanzu, tana nazarin lamarin da ke faruwa a Najeriya tare da duba abubuwan da suka faru kafin ta yanke hukuncin ƙarshe.

Hukumar ta kuma nuna cewa za ta ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa ta Najeriya kafin ta yanke hukuncin.

A cewar FIFA, tattaunawar da aka tsara za ta haɗa da wakilan CAF, da Hukumar Wasanni ta Ƙasa, wakilan gudanarwar NFF ta yanzu da kuma wakilan mambobin NFF daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *