Ƙungiyar Kano Pillars ta lallasa Niger Tornadoes da ci 3-2 a wasan mako na biyu na Gasar Firimiyar Najeriya ta (NPFL) a wasan da suka buga a ranar Lahadi, a filin wasa na Sani Abacha  dake KofarMata, Kano, a ranar Lahadi.

Pillars, wadda ake mata laƙabi da ‘Sai Masu Gida’, ta zura ƙwallaye biyu da nema ta hannun John Ubong Friday a minti na 40 da kuma ƙwallon da Fabian Nworie ya ci a minti na 45 kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Dawowa daga hutun rabin lokaci ke da wuya, mai masaukin baƙi ta ƙara zura ƙwallo ɗaya a raga, inda Fabian Nworie ya zura ƙwallonsa ta biyu a karawar.

Niger Tornadoes ta canza akalar wasan, yayin da ta farfaɗo daga baya inda ɗan wasa Joseph Godfrey ya nuna ƙwazonsa ya zura ƙwallo biyu shi kaɗai a mintuna na 72 da kuma 88.

Tornadoes ta yi ƙoƙarin farke duka ƙwallayen da aka zura mata, amma Pillars ta jajirce wajen tabbatar da samun narasa a fafatawar, inda a yanzu take mataki na uku da maki huɗu a teburin Gasar Firimiyar Najeriya.

A wani wasan na daban, ƙungiyar Plateau United ta garin Jos, ta doke Kwara United da ci 1-0 mai ban haushi a wasan da suka buga a sabon filin wasa na garin Jos, a ranar Lahadi.

Tun a minti na 29, ɗan wasa Alex Aghahowa Otakho, ya zura ƙwallon da ta bai wa mai masaukin baƙi nasara duk da hare-haren da Kwara United ta kai domin farke cin da aka yi mata.

A garin Lafiya, bayan shan kaye a wasan farko, Nasarawa United ta doke Bendel Insurance da ci 1-0 inda ta haɗa maki uku daga wasanni biyu da ta buga.

Ɗan wasa Pam Samuel, ne ya zura ƙwallon da ta tabbatar wa masu masauƙin bakin nasara a minti na 55.

Ga cikakken sakamakon wasannin da aka buga na ranar Lahadi, na mako na biyu na Gasar Firimiyar Najeriya:

Kano Pillars 3-2 Niger Tornadoes

Kun Khalifat 0-0 Barau FC

Nasarawa United 1-0 Bendel Insurance

Plateau United 1-0 Kwara United

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *