Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirika, ta yi maraba da ƙarin tallafin da gwamnatin Birtaniya ta amince da bayarwa domin taimakawa wajen yaƙi da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, DRC.

Tallafin  jimillar kuɗin da Birtaniya ta ware don wannan batu ya kai fam miliyan 78.7.

Wannan ƙarin tallafi na zuwa ne a lokacin da hukumomin lafiya ke ƙara ƙaimi wajen dakile yaɗuwar cutar Ebola zuwa wasu ƙasashen Afirka.

Cibiyar CDC ta ce tallafin zai taimaka wajen ƙarfafar matakai na gano masu ɗauke da cutar cikin gaggawa, damin ba su magani da kare ma’aikatan lafiya da al’ummomin da ke cikin haɗari.

Sanarwar ta biyo bayan wata ganawa da Darakta-Janar na cibiyar CDC, Dakta Jean Kaseya, ya yi da Ministar Birtaniya mai kula da raya ƙasashe, Kirsty McNeill, a Addis Ababa a makon da ya gabata.

Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a shawo kan Ebola, da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin, da kuma tabbatar da cewa ƙasashen da abin ya shafa sun samu tallafi na tsawon lokaci.

Da take jawabi a Majalisar Wakilan Birtaniya, Ministar McNeill ta ce ƙasar ta na goyon bayan yadda ƙasashen Afirika ke jagorantar matakan da ake ɗauka domin yaƙi da cutar. Sannan ta kuma bayyana muhimmancin rawar da Cibiyar Afirika CDC ke takawa wajen haɗa kan ƙasashen yankin domin dakile cutar.

Dakta Kaseya ya ce suna tare da gwamnatin Kongo, maƙotan ƙasashe da sauran abokan hulɗa domin dakatar da yaɗuwar cutar. Ya kuma jaddada cewa jagorancin Afirika, tare da goyon bayan ƙasashen duniya, na da muhimmanci wajen samun nasara a yaƙi da annobar.

Za a yi amfani da ƙarin kuɗin wajen tallafa wa ayyukan yaƙi da Ebola a DRC da Uganda, da kuma ƙarfafa shirye-shiryen ƙasashen yankin na fuskantar cututtuka masu yaɗuwa.

Daga cikin ayyukan akwai sa ido kan cututtuka, ƙarfafa dakunan gwaje-gwaje, rigakafin kamuwa da cuta, kula da marasa lafiya, wayar da kan al’umma da kuma ƙara shirin tunkarar barazanar da ka iya tasowa a kan iyakokin ƙasashe.

Dakta Kaseya ya gode wa gwamnatin Birtaniya bisa ci gaba da tallafawa yaƙi da yaduwar annobar, yana mai cewa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da ya dace da bukatun ƙasashen da abin ya shafa shi ne hanya mafi dacewa ta shawo kan annobar da kare rayukan jama’a da ma’aikatan lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *