Tawagar Super Eagles ta Najeriya

Najeriya da Russia za su sake haɗuwa a karo na biyu cikin watanni 16, yayin da za su buga wasan sada zumunta na ƙasa da ƙasa a filin wasa na Nizhny Novgorod a ranar Talata, 6 ga watan Oktobar 2026.

Wakilin Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, a Najeriya, Pachon na Eurodatasports, ne ya tabbatar da hakan.

Idan za a iya tunawa dai, ƙasashen biyu sun tashi kunnen doki ci 1-1 a wani wasan sada zumunta da suka buga a filin wasa na Luzhniki da ke Moscow a ranar 6 ga watan Yunin 2025.

Kuskuren da ɗan wasan baya, Semi Ajayi, ya yi na cin gida shi ya bai wa masu masaukin baƙi damar fara zura ƙwallo a rabin farko na wasa, amma Najeriya ta farke ƙwallon a rabi na biyu ta hannun Tolu Arokodare.

Wannan wasan sa da zumunta zai gudana ne mako ɗaya bayan wasan neman tikitin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka, AFCON, ta 2027 na wasa ta biyu tsakanin Super Eagles da Guinea Bissau, a Bissau ranar Talata, 29 ga Satumba.

Najeriya za ta fara fafata wasan neman shiga Gasar AFCON ta 2027 kwanaki huɗu kafin hakan da ƙasar Madagascar a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.

A halin yanzu, Super Eagles ta na matsayi na 26 a jadawalin FIFA na duniya, yayin da Russia ke matsayi na 35.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *