Tawagar Falconets ta Najeriya ta sha kaye a hannun ƙasar Spaniya a ranar Litinin, a wasansu na farko na rukunin F na Gasar Cin Kofin Duniya na Mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 da suka buga a Sosnowiec, dake ƙasar Poland.
Spaniya ta nuna ƙwarewarta ta fuskar amfani da damarta da yadda ta buga salon wasa na haɗin kai tsakanin ‘yan wasan, hakan ya sa ta cancanci samun nasara a karawar.
Yayin da ‘yan wasan Najeriya suka nuna irin tasu ƙoƙarin sai dai sun buga salon wasa ne na miƙa ƙwallaye daga tsakiya, amma ba su samu damar kai hare-haren matsin lamba wa masu tsaron gidan Spaniya sosai ba.
-
UEFA za ta girmama waɗanda ambaliyar ruwa ta kashe a Nepal kafin wasanni
-
NPFL: Kano Pillars da Plateau United da Nasarawa United sun yi nasara a gida
-
Shooting Stars ta lallasa CS Sfaxien a wasan farko na Gasar CAF Confederation Cup
Spaniya ta fara zura ƙwallo a minti na 13 ta hannun Marisa Garcia.
Sannan ta ƙara ta biyu a minti na 73, lokacin da Alba Cerrato ta buga ƙwallo mai ƙarfi daga gefe ta shiga ragar mai tsaron ragar Najeriya, Ijeoma Uzoma.
Falconets za ta kara da ƙasar Sin a ranar Alhamis, kafin su buga wasansu na ƙarshe na rukuni da New Caledonia.