Dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai hare-hare kan jiragen ruwa 20 na Amurka da ke kokarin ratsa mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar man fetur da iskar gas ta duniya.
Iran ta kuma ce ta kai harin makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka na Al-Azraq da ke Jordan, a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da Amurka ta kai kan jiragen dakon man Iran.
A cewar kafar yada labaran kasar, IRNA, harin ya lalata wuraren gyaran jiragen yaki, wuraren jibge sojoji da kuma mafakar jiragen saman yaki.
Sai dai rundunar sojin Jordan ta ce ta kakkabo makamai masu linzami 18 da Iran ta harba zuwa cikin kasar.
Rikicin na baya-bayan nan ya biyo bayan wani hari da sojojin Amurka suka kai kan wasu jiragen dakon man Iran, inda Amurka ta ce ta lalata jiragen dakon mai guda biyar.
- Iran ta kai hari kan wani jirgin ruwa mara matuki na sojin Amurka a Mashigar Hormuz
-
Iran ta ce hare-haren Amurka sun kashe mutane huɗu a wajen bikin aure
-
Shin matsin lambar tattalin arziki daga Amurka zai sa Iran ta mika wuya?
Iran ta kuma gargadi jiragen dakon man da ke kusa da Kuwait da Bahrain, kasashen da ke kawance da Amurka, da su bar yankin, tana mai cewa za a iya kai musu hari.
A halin yanzu, Amurka da Iran na cikin wani yanayi na rashin jituwa da mako shida bayan fara yakin, yayin da Iran ke ci gaba da rike babban tasiri kan mashigar Hormuz, ita kuma Amurka ke kokarin takaita hanyoyin samun kudaden shiga da jigilar kayayyaki zuwa Iran.
Ci gaba da rikicin ya fara shafar kasuwannin duniya, inda farashin danyen man Brent ya tashi zuwa kusan dala 100 kan kowace ganga a kasuwannin Asiya.
Masana na ganin cewa idan aka ci gaba da samun cikas wajen jigilar man fetur ta mashigar Hormuz, hakan na iya kara dagula farashin makamashi tare da haifar da matsin lamba ga tattalin arzikin kasashen duniya.