Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta bayyana cewa za ta haɗa kai da hukumomin tsaro a jihar Nasarawa domin tabbatar da an kiyaye ƙa’idojin kamfen da dokokin zaɓe gabanin zaɓen ƙasa na shekarar 2027.

Kwamishinan Zaɓe na Hukumar a jihar Nassarawa, Muhammed Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin taron Kwamitin shawara kan tsaron zaɓe na cikon Giɓi da aka gudanar a garin Lafia.

Ya bayyana cewa hukumar za ta yi aiki kafada kafa da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa da ɗambin ƴan takara sun bi dokokin kamfen sau da ƙafa, da nufin samar da ingantacce kuma lafiyayyen yanayi na zaman lafiya ga dukkan ɓangarori.

Kwamishinan ya ƙara da cewa dole ne kamfen na siyasa ya kasance mai ma’ana da fa’ida da ya dace da tanadin dokokin zaɓe da ƙa’idojin hukumar INEC.

“Baza mu ɗauki kalaman ƙiyayya, tunzura jama’a, cin zarafi ko tashin hankalin siyasa, da lalata dukiyoyin gwamnati ba, kamar yadda tsarin mulki da dokar zaɓe suka tanada,” in ji shi.

Haka zalika, Kwamishinan ya jaddada cewa inganci da sahihancin zaɓe ya dogara ne kacokam kan yanayin da aka gudanar da shi.

“Dole ne masu ƙada ƙuri’a su ji cewa suna cikin aminci da tsaro domin gudanar da hakkin su na zaɓe, kuma dole ne a tsara tsaron ma’aikatan zaɓe don su gudanar da ayyukansu ba tare da fargaba ko razani ba,” in ji shi.

Daga ƙarshe, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kasance masu hange wajen sa ido kan kamfen na siyasa, da kuma kama duk wanda ya karya doka, ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *