Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin biyan alawus din kayan koyo da koyarwa ga Malaman Makarantun gaba da sakandire, na watanni 6, daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2026.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, jim kadan bayan kaddamar da kwamitin tabbatar da nagartar Makarantu na kasa a Abuja.
Alawus din ‘CATA’, wani tallafi ne da ake bai wa malamai domin tallafa musu wajen siyen kayan koyo da koyarwa.
Alausa, ya ce biyan kudaden na cikin yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2025, tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU).
“Gwamnatin Tarayya ta fitar da dukkanin kudaden na alawus din CATA, na watannin Janairu zuwa Agusta 2026 ga dukkanin Malaman jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da na ilimi.” Inji Alausa
Ministan ya kara da cewa, yanzu haka ana tsaka da gudanar da tsarin biyan ma’aikatan Makarantun gaba da sakandire (NASU).
A cewar Alausa, biyan kudaden wata alama ce ta fili da ke nuna jajircewar Gwamnati wajen cikar alkawarin da aka dauka. Inganta walwala da jin dadin ma’aikatan da suke koyarwa da wadanda ba malamai ba a manyan makarantun gaba da sakandire na kasar.
Daga karshe, ya jinjina wa Shugaba Tinubu bisa abin da ya bayyana a matsayin gagarumin shiri na sauya fasalin fannin ilimi.