Jihohi bakwai na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya sun nuna damuwa kan karuwar cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu da ke aiki ba tare da cika ka’idojin da suka dace ba a yankin, inda suka yi gargadin cewa lamarin na barazana ga rayukan jama’a.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Jigawa kuma shugaban ƙungiyar kwamishinonin lafiya na jihohin Arewa maso Yamma, Dakta Abdullahi Kainuwa, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.
Da yake jawabi ga shugabannin makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya a jihar, kwamishinan ya ce ƙungiyar na sane da yadda wasu cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ke gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida da ƙa’idojin da aka gindaya ba.
-
FRSC ta ƙaddamar da yunƙurin kawo ƙarshen lodin wuce kima
-
Shugabannin matasa Sun yi kira ga ‘yan siyasa su rungumi juriya yayin da za fara zaɓukan 2027
Ya ce hakan ba zai ci gaba da zama abin karɓa ba, inda ya bayyana cewa an kafa wani kwamiti na musamman da zai sa ido kan cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu domin tabbatar da cewa suna aiki bisa ƙa’idojin da suka dace.
Ya ce: “Duk makarantar da ba ta cika ƙa’idar da ake buƙata ba, mun bai wa kwamitin umarnin rufe ta.”
Ya ƙara da cewa aikin tantance makarantun yana gudana a dukkan jihohi bakwai na yankin Arewa maso Yamma.
Kwamishinan ya ce abin takaici ne yadda wasu daga cikin makarantun ba su da wurin zama na dindindin, da ma’aikatan dindindin,da dakunan gwaje-gwaje da sauran abubuwan da ake buƙata domin gudanar da irin wannan makaranta.
Ya ce gwamnati ba ta da isassun makarantu da za su iya ɗaukar yawan jama’ar da ke buƙatar ilimin kiwon lafiya, don haka akwai buƙatar makarantu masu zaman kansu, amma dole ne su kasance makarantu na gaskiya kuma su cika dukkan ƙa’idojin da aka gindaya.
Dakta Kainuwa ya kuma ce za a ɗauki mataki kan hukumomin da ke kula da harkokin makarantu idan aka gano cewa sun bayar da lasisi ga makarantu ba tare da sun tabbatar da wuraren karatu, ma’aikata, kayan aiki da sauran abubuwan da ake buƙata ba.