Attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, ya ce ba ya son a sake rika bayyana shi a matsayin attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar, yana mai cewa ya fi son a san shi da wanda ke samar da arziki da damarmaki ga sauran mutane.
Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 14 ga Satumba 2026, yayin da yake kaddamar da sayar da hannayen jarin kamfanin man ga jama’a, wato IPO, a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya da ke Legas.
Ya ce: “Ba na son kowa ya sake kirana da attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka. Ina son a kira ni mutumin da ya fi kowa samar da arziki a Afirka, domin in samar da arziki ga wasu.”
- Wane ne marigayi Bamanga Muhammad Tukur?
-
Ban taɓa ɗaukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane ba–Sanata Buba
Attajirin ya bayyana cewa sayar da hannayen jarin matatar man Dangote ya bai wa ‘yan Najeriya da sauran ‘yan Afirka damar shiga kai tsaye wajen samar da arziki ta hanyar mallakar hannayen jarin kamfanin.
Ya ce: “A yau, ba hannayen jari kawai muke bayarwa ba. Muna bayar da dama ne ga mutane su kasance cikin wani muhimmin sauyi da zai shafi tattalin arzikin Najeriya da ma Afirka baki daya.”
Dangote ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi kasuwar hada-hadar hannayen jari, yana mai cewa yawan shiga cikin kasuwar zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da samar da wadata.
Ya ce gina babbar daular kasuwancinsa ya bukaci sadaukarwa da juriya, inda ya gode wa ‘ya’yansa mata, Mariya, da Halima da Fatima, bisa irin goyon baya da fahimtar da suka nuna masa tsawon shekaru.