Tawagar Falconets ta Najeriya za ta kara da Young Lionesses ta Ingila a wasan zagaye na 16 na Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 a Poland a ranar Alhamis, 17 ga Satumbar 2026, don neman gurbi a wasan kwata-fainal.
Za a buga wannan wasa ne a filin wasa na Stadion Miejski Bielsko-Biała, da misalin ƙarfe 2:00 na rana agogon Najeriya.
Falconets, ƙarƙashin jagorancin koci Moses Aduku, ta tsallake zuwa zagaye na 16 bayan gagarumar nasarar da ta samu na cin ƙwallaye 10-1 a kan New Caledonia a wasanta na ƙarshe na Rukunin F.
Da farko, Najeriya ta sha kashi a hannun Spaniya da ci 2-0, sannan kuma ta yi canjaras 0-0 da China.
-
Taron NFF: Tawagar FIFA da CAF ta kammala tattara bayanai ta koma Zurich
-
Nairobi ta kada Landan wajen neman karɓar baƙuncin Gasar Motsa Jiki ta Duniya
-
Sabon Kocin Senegal Patrick Vieira ya magantu
Ramotalahi Kareem da Onajite David, kowannen su, ta ci ƙwallo uku-uku yayin karawa da New Caledonia.
Falconets ta taɓa zuwa wasan ƙarshe sau biyu na wannan gasa, inda take kammalawa a matsayi na biyu a shekarun 2010 da 2022, koda yake har yanzu tana neman kambunta na farko.
A nata ɓangaren, Young Lionesses ta Ingila ta kammala wasannin rukunin B a matsayi na biyu.
Ta lallasa Tanzania da ci 5-1 ta tashi kunnen doki 1-1 da Canada, sannan kuma ta sha kaye ci 2-1 a hannun Brazil.
‘Yar wasan baya Rachel Maltby ta kasance daga cikin fitattun ‘yan wasan Ingila a matakin rukuni, inda ta ci ƙwallaye uku (hat-trick) a kan Tanzania.
Yanzu da tawagun biyu suka shiga matakin da za a fitar da wadda ta yi rashin nasara kai-tsaye, wasan na ranar Alhamis na da matuƙar muhimmanci.
Wanda ya yi nasara zai tsallake zuwa wasan kwata-final.
Haɗuwar da suka yi a baya
Najeriya da Ingila sun taɓa haduwa a Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ‘yan ƙasa da shekaru 20 inda suka buga wasanni masu ƙayatarwa.
Tawagun sun buga kunnen doki 1-1 a 2008 da 2010, kafin Najeriya ta samu nasara 2-1 a 2014.
A wancan haduwar, Asisat Oshoala ta ci bugun fenareti mai cike da nasara bayan Loveth Ayila ta farke ƙwallon da aka zura wa Najeriya.
Wannan karawa da tawagun biyu za su yi na ranar Alhamis ta ƙara wani babi a tarihin da ke tsakanin ɓangarorin biyu, inda Falconets ke fatan samun sakamako mai kyau a kan Young Lionesses don samun tikitin wasan kwata-fainal.
