Tawagar Najeriya ta fara yaƙin neman lashe Gasar Ƙwallon Raga ta Maza ta Ƙasashen Afirka ta 2026 da ƙafar dama yayin da ta doke Chadi 3-0 (25-17, da 25-17, da kuma 25-6) a Tunisia a ranar Laraba, 16 ga Satumba.

Najeriya na burin samun tikitin shiga Gasar Olympics da za a yi a Los Angeles a 2028, tare kuma da samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta FIVB ta 2027.

Zakarun yankin na Shiyya ta 3 sun mamaye zagayen farko na wasan, inda suka doke Chadi 25-17 kafin suka sake maimaita irin wannan maki a zagaye na biyu.

Tawagar Najeriya ta kammala aikin a zagaye na uku, inda ta yi nasara da 25-16 don tabbatar da nasararta ta farko a gasar.

Da yake magana bayan nasarar, babban kocin kungiyar kwallon raga ta maza ta Najeriya, Ryan Masajedi ya yaba wa ‘yan wasansa saboda aiwatar da tsarin wasan da aka tsara akan Chadi.

Kocin ya ƙara da cewa a yanzu tawagar za ta mayar da hankali ne kan wasanta na gaba na rukuni da Algeria.

“Na yi farin ciki da cewa ‘yan wasan sun buga abinda aka ce suyi; hakan na nuna horar da muka basu na aiki yayi kyau,” in ji shi.

Masajedi ya kuma yaba wa ‘yan Najeriya a gida saboda goyon baya da hadin kan da aka baiwa tawagar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *