Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) ta gudanar da gagarumin samame a wuraren da aka gano a matsayin maboyar masu aikata laifuka, gidajen kwana da kuma gine-ginen da ba a kammala ba a sassa daban-daban na Abuja.

An gudanar da samamen ne a ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, a wani mataki na dakile aikata laifuka, tarwatsa maboyar masu laifi da kuma inganta tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna FCT.

A cewar rundunar, jami’an tsaro sun kai samame a wurare daban-daban da ake zargi da zama maboyar masu aikata laifuka, inda suka kama kimanin mutane 300.

Daga cikin abubuwan da aka kwato yayin aikin akwai wuƙaƙe da bindiga da tabar wiwi da wasu haramtattun ƙwayoyi.

Rundunar ta ce ana ci gaba da tantance mutanen da aka kama, inda za a gurfanar da duk wanda bincike ya tabbatar da aikata laifi a gaban kotu bisa tanadin doka.

Haka kuma, za a saki waɗanda aka tabbatar ba su da wata hujjar da za ta sa a ci gaba da tsare su.

Kwamishinan ’Yan Sandan FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da samame bisa bayanan sirri da kuma ayyukan dakile laifuka, musamman a wuraren da aka gano cewa masu laifi na amfani da su a matsayin maboya.

Kwamishinan ya kuma gargadi matasa da sauran mazauna Abuja kan amfani da haramtattun ƙwayoyi, yana mai cewa shaye-shayen ƙwayoyi na iya cutar da hankalin mutum da kuma haifar da tashin hankali da aikata laifuka, tare da jefa al’umma cikin matsalolin tsaro.

Rundunar ’Yan Sandan FCT ta sha gudanar da samame a wuraren da ake zargi da zama maboyar masu laifi a Abuja a cikin watan Satumba, ciki har da samamen da ya kai ga kama mutane 70 a yankin Unity Fountain da Maitama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *