Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen Jihar Kano, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara kulawa da al’ummarFulani makiyaya tare da sanya su cikin shirye-shiryen ci gaban jihar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin martaninsa kan kiran da Gwamnan Kano ya yi na inganta rayuwar al’ummomin Fulbe ta hanyar samar da ilimi, tallafin jari, ruwan sha, kiwo da sauran abubuwan more rayuwa.
Ya ce duk da jin wannan kira, abin da ke damun al’ummar makiyaya shi ne yaushe za a fara ganin wannan kulawa a aikace.
- Ranar Muhalli ta Duniya 2026: Masu Ruwa da Tsaki a Kaduna Sun Hadu don Samar da tsaftataccen Muhalli
- NMDPRA: Ba mu ne ke kayyade farashin man fetur a gidajen mai ba
- 2027: Ku mutunta tsarin karɓa-karɓa ta hanyar goyon bayan Tinubu – ƙungiya
Ya bayyana cewa a matsayinsa na Shugaban MACBAN na Kano, yana wakiltar makiyaya da masu kiwo a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
A cewarsa, sun sha neman damar ganawa da Gwamnan Kano da Mataimakinsa domin gabatar da matsalolin al’ummarsu, amma har yanzu ba su samu damar zama da su domin tattaunawa ba, duk da cewa hakan ya shafe tsawon shekaru biyu zuwa uku.
Shugaban MACBAN ya ce suna ganin ana tallafa wa ƙungiyoyin manoma da mahauta da mafarauta da sauran ƙungiyoyi a jihar, yana mai cewa ba sa adawa da irin wannan tallafi.
Sai dai ya tambayi dalilin da ya sa ba a bai wa makiyaya irin wannan dama da kulawa ba.
Ya ce halin da ake ciki ya sa wasu daga cikin al’ummarsu ke tambayar shugabanninsu inda za su koma, ganin cewa gwamnati ba ta saurare su ba, balle ta tallafa musu.
Ya kuma yi watsi da zargin cewa shugabannin makiyaya suna karɓar tallafi daga gwamnati suna cinye wa mabiya, yana mai cewa shi kansa bai taɓa karɓar ko naira ɗaya daga gwamnatin jihar Kano ba.
Saboda haka, ya yi kira ga gwamnatin Kano da ta buɗe ƙofa ga ƙungiyar Miyetti Allah domin tattaunawa, tare da shigar da makiyaya cikin shirye-shiryen gwamnati.
Ya jaddada cewa makiyaya ma ’yan Kano ne, kuma suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar tattalin arzikin jihar da harkokin siyasar jihar, musamman la’akari da yawan al’ummar makiyaya da ke zaune a Kano.