Raphinha ya zura Ƙwallaye uku yayin da Barcelona ta dawo daga baya ta doke Sevilla da ci 3-1, a wasan LaLiga da aka fafata ranar Asabar.
Sevilla ce ta fara samun nasara, bayan Youssouf Fofana ya zura ƙwallo a minti na 19.
- Salah ya zura ƙwallaye uku, yayin da Trabzonspor ta ragargaji Galatasaray
- Ana zargin wata mata ta kashe mijinta saboda zai kara aure na biyu a Kano
Sai dai Raphinha ya farke bayan mintuna uku, kafin ya ƙara wasu ƙwallaye biyu bayan an andawo hutun rabin lokaci.
Nasarar ta sa Barcelona ta ci gaba da samun cikakkiyar nasara a gasar, inda yanzu ta lashe wasanni bakwai a jere, kuma take saman teburin LaLiga da tazarar maki shida.