Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta nesanta kanta da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa (PCC) da ƙungiyar Obi-Kwankwaso (OK Movement) ta kafa ranar Alhamis.
Jam’iyyar ta ce ba ta amince da kafa kwamitin ba, tare da yin kira ga jama’a da kafafen yaɗa labarai da su yi watsi da sanarwar.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, OK Movement ta sanar da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen mai mambobi 59 ranar Alhamis, gabanin zaɓen 2027.
- NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi da aka kiyasta ya kai Naira biliyan 3.4 a jihohi takwas
- Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Kwamitin Bikin Cika Shekaru 66 da samun ‘yancin kai
- Mashako na ƙara yaɗuwa a Najeriya: Me ya sa cutar da ake iya rigakafi ke ci gaba da kashe mutane?
NAN ya ruwaito cewa an naɗa John Ughulu, a matsayin Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen, yayin da aka kuma saka Sakatariyarsan, Saadatu Sani, cikin shugabannin yaƙin neman zaɓen.
Kwamitin ya kuma ƙunshi masu kula da shiyyoyi da jihohi, da daraktocin wayar da kan jama’a, harkokin mata da dabarun yaƙin neman zaɓe da tsaro da harkokin shari’a da sauran muhimman fannoni.
Sai dai Shugaban NDC, Sanata Moses Cleopas, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce ya kamata a yi watsi da kwamitin da aka sanar.
Cleopas ya ce shugabancin jam’iyyar ne kaɗai ke da ikon kafa tare da sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.
Ya ƙara da cewa babu wani mutum, ɗan takara ko ƙungiyar magoya baya da aka ba izinin ƙirƙira ko bayyana tsarin yaƙin neman zaɓe da sunan jam’iyyar ba tare da amincewar Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) ba.
Cleopas ya ce NDC na ci gaba da mai da hankali kan yaƙin neman zaɓe bisa batutuwa da manufofi, da kuma ƙudurin samar da abin da ya kira “Sabuwar Najeriya da za ta yiwu.”