Shugaban Rundunar Sojojin Ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ƙaddamar da motocin aiki da aka a Bataliya ta 1 ta Mata da ke Giri, Abuja.
Rundunar ta ce matakin na da nufin ƙara inganta zirga-zirgar sojoji da saurin mayar da martani ga buƙatun ayyukan tsaro da kuma walwalar jami’an soji.
Da yake jawabi a bikin da aka gudanar ranar Litinin, 21 ga Satumba, 2026, shugaban rundunar, wanda Mukaddashin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Ƙasa, Kanal Appolonia Anele, ya wakilta, ya ce motocin aiki masu kyau na da muhimmiyar rawa wajen jigilar jami’ai, kayan aiki da sauran kayayyakin da ake buƙata cikin gaggawa.
- Tinubu ya tsawaita hutun aiki har zuwa karshen mako
- Wike zai bayyana dalilin adawa da Rainbow Coalition
- NAF ta fara sayen jirage masu saukar ungulu 12 kirar AH-1Z Viper
Ya ce ingancin ayyukan soji yana da alaƙa da samuwar kayan aiki masu kyau da kuma tabbatar da cewa motocin da rundunar ke amfani da su suna cikin yanayin da ya dace.
Laftanar Janar Shaibu ya umurci kwamandoji da jami’an da aka damƙa musu motocin da su tabbatar da kula da su yadda ya kamata, tare da amfani da su bisa ƙa’idojin rundunar.
Ya jaddada cewa motocin kadarorin ƙasa ne, don haka dole ne a kare su, a basu cikakkiyar, sannan za a yi amfani da su ne kawai wajen ayyukan soji da aka amince da su.
Game da Nightingale Club, shugaban rundunar ya ce cibiyar wata muhimmiyar gudummawa ce wajen inganta walwalar sojoji, saboda rundunar da ke da ƙwarewa da juriyar aiki tana buƙatar yanayi da zai tallafa wa jin daɗin jami’anta.
Tun da fari, Birgediya Janar Muhammed Sani Adamu, ya bayyana Nightingale Club a matsayin wani muhimmin jari wajen inganta walwalar jami’an soji.
Birgediya Janar Adamu ya yaba wa shugaban rindunar sojin bisa jagorancinsa da kuma ci gaba da samar da albarkatun da ke inganta walwalar jami’an soji, bisa tsarin soji a farko daya kirkiro dashi.