Rahotanni sun ce an kashe mutane uku a birnin Minna na Jihar Neja, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan daba suka yi a yankin Kpakungu na birnin.
An ce ’yan daban sun fito kan tituna ne a ranar Lahadi, domin nuna adawa da kisan wani daga cikinsu mai suna Aliyu, wanda wasu jami’an sa-kai suka kashe yayin da suke ƙoƙarin kama wasu ’yan daba a yankin Kpakungu na Minna a ranar Asabar, 3 ga Oktoba, 2026.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi.
- An kama mutum biyu kan zargin cin zarafin ’yan sanda a Bauchi
- Musawa ta bai wa Tinubu hoton da ta zana shi da mahaifiyarsa
- SERAP ta bukaci a yi bincike kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan 94.4 na man fetur
Ya ce da misalin ƙarfe 10:30 na dare ranar 3 ga Oktoba, 2026, rundunar ta samu rahoton cewa wasu jami’an sa-kai sun taru a yankin Kpakungu domin kama wasu ’yan daba.
SP Abiodun ya ce yayin da ake ƙoƙarin kama ’yan daban, ɗaya daga cikin jami’an sa-kan ya harbe wani mai suna Aliyu har lahira, lamarin da ya haddasa zanga-zanga a yankin.
Ya ce an tura jami’an sintiri zuwa wurin, inda suka shawo kan lamarin tare da dawo da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin cafke jami’in sa-kan da ya yi harbin.
A cewar kakakin ’yan sandan, wasu daga cikin ’yan daban sun sake haɗuwa da sassafe ranar 4 ga Oktoba, 2026, inda suka tare hanyar Bida zuwa Minna da sunan zanga-zanga.
Ya ce daga bisani sun nufi yankin Gbeganu, inda suka kai wa mazauna yankin hari.
SP Abiodun ya ce a yayin harin, an samu rahoton mutuwar wasu mutane biyu.
Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa an tura jami’an rundunar dabarun yaƙi zuwa yankin, inda suka tarwatsa masu tayar da hankalin tare da bude hanyar domin zirga-zirgar ababen hawa ta ci gaba.
