Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce ta aika allunan lambobin rajistar motoci guda 19,560 zuwa Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, a cikin watan Oktoba na shekarar 2026.

Hukumar ta bayyana cewa ta aika allunan lambobin motoci guda 15,205 a ranar 8 ga Oktoba, waɗanda suka haɗa da na motoci masu zaman kansu guda 15,169, na musamman guda 32 da kuma guda huɗu da ba sa cikin jerin lambobin da aka saba amfani da su.

A ranar 20 ga Oktoba, hukumar ta sake aika wasu allunan lambobin motoci guda 4,355, ciki har da na motoci masu zaman kansu guda 1,998, na kasuwanci guda 999, na gwamnatin birni guda takwas, na dillalan motoci guda 900 da na manyan motocin dakon kaya guda 450.

FRSC ta ce ta fitar da waɗannan bayanai ne domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da fayyace bambanci tsakanin ƙera allunan lambobin motoci da aika su ga hukumomin rajista, da kuma matakan da ake bi kafin miƙa su ga masu motoci.

Hukumar ta amince cewa wasu mutane na iya fuskantar jinkiri wajen karɓar allunan lambobin motocinsu bayan kammala rajista, amma ta ce hakan na buƙatar ingantaccen haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke da alhakin rajistar ababen hawa.

Shugaban hukumar, Shehu Mohammed, ya ce FRSC za ta ci gaba da haɗin gwiwa da hukumomin bayar da lasisin ababen hawa na jihohi da sauran hukumomin da abin ya shafa domin rage cikas da inganta ayyukan rajista.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *