Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation WHIRL STROKE sun fatattaki wasu da ake zargin masu aikata laifuka ne, tare da kwato bindigogin AK-47 guda biyu a Ƙaramar Hukumar Guma ta Jihar Benuwe.

A cikin sanarwar da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, ya fitar ranar 26 ga Oktoba, 2026, ya ce dakarun sun gudanar da samamen ne bisa sahihan bayanan sirri kan wasu da ake zargin masu laifi ne, waɗanda suka shigo Guma daga Jihar Nasarawa.

Sanarwar ta ce bayan isar dakarun wurin, mutanen sun buɗe musu wuta, amma sojojin suka mayar da martani tare da tilasta musu tserewa, sai dai a a samu asarar rai a tsakanin sojojin ba.

Bayan fatattakar maharan, dakarun sun kwato bindigogin AK-47 biyu, guraben cajar bindiga guda huɗu, ’yan maruƙa takwas, wayoyin hannu uku, takardar lambar shaidar ɗan ƙasa ta NIN mai ɗauke da sunan Umar Yusuf, da kuma kuɗi Naira 20.

Kwamandan rundunar haɗin gwiwar, wanda kuma shi ne Kwamandan Rukunin Sojoji na 5, Manjo-Janar Moses Kolo Gara, ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewarsu da kuma yadda suka mayar da martani cikin gaggawa.

Ya buƙaci sojojin su ƙarfafa haɗin gwiwa da al’ummomin yankin, sannan ya gode wa jama’a bisa samar da bayanan sirri.

Kwamandan ya kuma yi kira ga mazauna yankin su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko aiki da suke zargi domin taimakawa wajen dakile laifuka da inganta tsaro.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *