Idris ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Minna, Jihar Neja, yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan jihar na APC, wanda Gwamna Mohammed Umaru Bago ya jagoranta.
- INEC ta buɗe rajistar masu zaɓe ta wucin gadi a intanet gabanin zaɓen 2027
- Gwamnan Neja ya ce APC na son samo wa Tinubu ƙuri’u miliyan biyu a 2027
Ministan ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ta aiwatar cikin shekaru uku da rabi sun fara magance matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar, tare da samar da damar bunƙasa tattalin arziƙi.
Ya ƙara da cewa shirin Renewed Hope Agenda na da manufar gyara matsalolin tattalin arziƙi, inganta kuɗaɗen gwamnati, jawo masu zuba jari da faɗaɗa manyan ayyukan more rayuwa.
Idris ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ayyukan gwamnatin tarayya da na gwamnonin APC za su kasance cikin manyan abubuwan da jam’iyyar za ta gabatar wa masu zaɓe a 2027.