Bago ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan jihar na APC mai mambobi 525, a Minna ranar Litinin.
- Rundunar Operation Hadin Kai ta ce ta kashe ’yan ISWAP 16 a hare-haren sama da ƙasa a Tafkin Chadi
- INEC ta buɗe rajistar masu zaɓe ta wucin gadi a intanet gabanin zaɓen 2027
Gwamnan ya ce jam’iyyar za ta yi amfani da tsarin tattara magoya baya daga rumfunan zaɓe zuwa matakin gundumomi, ƙananan hukumomi da jiha domin cimma wannan buri.
Ya bayyana cewa haɗin gwiwar siyasar da ke tallafa wa kamfen ɗin ta haura mambobi 100,000 a tsawon shekaru, abin da ya ce zai taimaka wajen shirya ayyukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar.
Bago ya kuma sanar da cewa za a ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a yankin Arewa ta Tsakiya da ke Minna a mako mai zuwa, inda ake sa ran manyan jami’an gwamnati da na jam’iyyar za su halarta.